✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata za su fara aikin soja a Saudiya

Rahotanni daga kasar Afirka ta Kudu na nuna da cewa wata Zakanya ta kashe wata mata a gidan kula da namun daji na birnin Pretoria…

Rahotanni daga kasar Afirka ta Kudu na nuna da cewa wata Zakanya ta kashe wata mata a gidan kula da namun daji na birnin Pretoria da ke kasar Afirka ta Kudu. 

Kakakin hukumar Netcare 911, wadda ke bayar da agajin gaggawa Nick Dollman, ya tabbatar da aukuwar lamarin sannan ya ce hukumarsa ta yi gaggawar kai dauki ga matan bayan da aka kira ta gidan namun dajin da ke garin Hammanskraal.

“Abin takaicin shi ne, matar ta samu munanan raunuka kuma nan take ta mutu,” in ji Mista Dollman.

Har yanzu dai babu wani cikakken bayani a kan abin da ya sa zakanyar ta kai wa matar hari hart a kashe ta.

Mr Dollman ya ce mutanen da suka je gidan kula da namun dajin ne suka kai wa matar, mai shekara 22, dauki ta hanyar daddanna kirjinta domin numfashinta ya dawo.