An bayyana irin gudunmawar da mata da matasa da shugabannin addini da sarakunan gargajiya za su iya bayarwa wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin manona da makiyaya da kuma tsakanin mabiya addinan da ke zaune a Kudancin Jihar Kaduna.
Farfesa Sunday B. Agang, na kungiyar ‘Peace Gathering’ ne ya bayyana haka yayin da yake karanto rahoton da suka tattara na jin ra’ayin jama’a don nemo mafita kan rikice-rikicen da suka addabi yankin.
Farfesa Agang ya yi kira ga malaman addinai su rika fada wa mabiyansu gaskiya tare da nuna musu muhimmancin zaman lafiya a masallatai da coci-coci, sannan ya yi kira ga matasa su guji yada munanan kalamai a kafofin sadarwa na zamani, maimakon haka su rika amfani da su wajen yada kalaman hadin kan kasa da jama’arta. “Gurbacewar tarbiyya da ke tasowa daga gida da lalacewar dangantakar da ke tsakanin mabiya addinai ta kai ga hatta idan aka taso daga makaranta sai ka ga Musulmi da Kirista sun ware kowa na tafiya da ’yan uwansa, wannan ba karamin barazana ce ga zamantakewa ba,” inji shi yayin da yake karanta rahoton.
Da ya waiwaya kan jami’an tsaro da gwamnati, ya yi kiran su rika zartar da hukuncin ba sani ba sabo ga duk wanda aka kama da laifi wajen haddasa fitina komai matsayinsa.
A karshe malamin ya yi kira ga gwamnati da sauran kungiyoyi da su rika samar wa matasa aikin yi don rage musu zaman kashe wando.
Shugaban zaman da Mataimakinsa, Rabaran Gideon Para-Mallam da Alhaji Muhammad Kabir kassim sun bayyana nisantar juna da rashin tattaunawa a matsayin abubuwan da suke haifar da kyamar juna.
Shugabannin biyu sun bayyana rashin adalci da jahilci da rashin aikin yi tare da gurbata karantarwar addinai a matsayin kadan daga cikin abubuwan da ke haifar da rashin zaman lafiya a cikin al’umma.
Da yake nasa jawabin, Shugaban Cocin Anglikan na Kudancin Kaduna, Bishop Markus Madugu Dogo cewa ya yi addinin Musulunci da na Kiristanci dukansu ba gado ba ne face dai wasu hanyoyi ne dan Adam ya zabar wa kansa bisa yarda da fahimta don gudanar da rayuwarsa a kai.
Bishop Markus, ya ce lokaci ya yi da za a fara ganin zaman lafiya a aikace, ba yawan surutu ba.
Taron, wanda aka gudanar da shi a dakin taro na Multi-Purpose da ke Unguwar Katsit a Kafanchan, ya samu halartar wakilai daga kungiyoyin mata da matasa da jami’an soji da ’yan sanda da malaman addinai da sarakunan gargajiya da sauran bangarorin jama’ar Musulmi da Kiristoci.