✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu zanga-zanga sun kone caji ofis a Neja

Masu zanga-zangar sun fusata ne kan sace-sacen ’yan bindiga a yankin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, wadanda suka yi zanga-zanga kan sace-sacen mutane da ’yan bindiga ke yi a yankin Gauraka na Karamar Hukumar Tafa a Jihar Neja, sun kone wani ofishin ’yan sanda.

Da safiyar yau ta Litinin ce masu zanga-zangar suka datse babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja don nuna bacin rai game da sace-sacen mutane da ake yi a yankin.

Rahotanni na cewa masu zanga-zangar sun fusata ne bayan wasu ’yan bindiga sun sace mutum kimanin 15 a yankin.

Aminiya ta ruwaito cewa, tuni dai jami’an tsaro da suka hada da ’yan sanda da dakarun soji suka tarwatsa masu zanga-zangar da suka tare hanyar da sanya matafiya da dama suka yi cirko-cirko.

Yayin ganawarsa da manema labarai, Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mutum shida ’yan bindigar suka sace sabanin 15 da aka ambato.

“Rundunar ’yan sandan jihar Neja, na tabbatar da cewar wasu ‘yan bindiga sun sace mutum shida a Angwan-Wazobia, wani gari a yankin Gauraka na Karamar Hukumar Tafa.

“An aike da jami’an ’yan sanda wurin da abun ya faru don ceto wanda aka yi garkuwa da su.

“Sai kuma da aka samu wasu marasa kishi da suka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda suka yi zanga-zangar sace-sace mutanen da aka yi a yankin.

“Daga bisani kuma masu zanga-zangar sun cinna wa caji ofis din Gauraka wuta tare da lalata abubuwa da yawa,” a cewar Abiodun.