✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu neman kowa wa zabe cikas su kuka da kansa

Shugaba Buhari ya ce, duk wanda ya yi yunkurin sace akwatin zabe ko tayar da rikici, to a bakin ransa

Rundunar Tsaro ta Najeriya ta ce ba za ta bata lokaci ba wajen sanya karfi ga duk wanda ya yi yunkurin kawo matsala a zaben shugaban kasa da ke tafe ranar Asabar.

Daraktan Yada Labaran Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, Birgediya Tukur Gusau ne ya sanar da haka a taron ’yan jarida kan al’amuran tsaro a Hedikwatar Tsaro a ranar Alhamis.

Matsayin sojojin ya zo daidai da kalaman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na cewa, “Duk wanda ya yi yunkurin sace akwatin zabe ko jagorantar ’yan daba, saboda takamar shi wani ne a yankinsu, to ya kwana da sanin cewa zai yi ne a bakin ransa.”

A zaman masu fada a ji na Jam’iyyar APC, an ji Buhari na cewa “duk wanda ya nemi kowa cikas ga zaben da ke tafe, to zai iya rasa rayuwarsa.

“Kada wani ya kuskura ya kawo tashin hankali, to zai gamu da gamonsa.

“Ma umarci sojoji da sauran hukumomin tsaro su dauki matakin da ya dace, kar su raga wa kowa, domin ba za mu yarda a zarge mu da yunkurin murdiyar zabe ba.

“So nake a mutunta ra’ayin ‘yan Najeriya, a bari su zabi duk wanda suka ga dama kuma a kowace jam’iyya.”

Mahalarta taron Hedikwatar tsaron sun hakda da kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Commodore Wap Maigida, kakakin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) Peter Afunanya; takwaransa na rundunar ’yan sanda, Olumuyiwa Adejobida sauransu.