✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu kwacen waya da sane sun shiga hannu a Taraba

’Yan sintiri sun cafke masu yankan aljihu da kwacen waya takwas a garin Jalingo na Jihar Taraba. Kwamandan kungiyar ’yan sintiri reshen Jalingo, Munir Bello,…

’Yan sintiri sun cafke masu yankan aljihu da kwacen waya takwas a garin Jalingo na Jihar Taraba.

Kwamandan kungiyar ’yan sintiri reshen Jalingo, Munir Bello, ya miyagun da suka addabi babbar kasuwar Jalingo da sauran sassan jihar sun shiga hannu.

Munir Bello ya ce dubun masu kwacen waya da yankan aljihu guda takwas ta cika ne a wani samame da ma’aikatansa suka kai a kwanan nan.

Kwamandan ya ce wadanda aka titsiye din sun yi fice a harkar sane da kwacen wayar hannu da kudade a hannun jama’a.

Daga cikinsu akwai samari masu kananan shekaru wanda a daren Talata suka kai hari kan wasu mata biyu a tsohuwar hanyar filin jirgin sama, inda suka kwace musu wayoyin da kudade.

Kwamandan ya ce an mika ababen zargin a hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike.

— An karrama ‘yan sintiri 100 a Taraba

A baya-bayan nan ne Mista Munir ya ba da lambar girma ga wasu ’yan bijilanti 100 a sakamakon kwazo da kwarewa da suka nuna tare da sadaukar da kai da agazawa sauran hukumomin tsaro wajen tsare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kirayi Gwamnatin Jihar da sauran masu kishin kasa da su ci gaba da goyon bayan ’yan kungiyar ta duk hanyar da ta dace.

Ya kuma yaba wa Gwamna Darius Ishaku dangane da gudunmuwar motocin sintiri da ya bai wa kungiyoyin bijilanti a jihar, lamarin da ya ce zai taka rawar gani wajen kara musu karsashi a kan aiki.

Kazalika, Mista Munir ya hori ’yan bijilanti da su kara jajircewa tare da aiki cikin tsoron Allah kuma su kasance jakadu na gari ga kungiyar.