Rahotanni daga Jihar Borno na cewa adadin masu kamun kifi da kungiyar Boko Haram ta kashe a lokaci guda a Jihar Borno ya karu zuwa 31, wasu sama da 40 kuma sun bace.
Da farko Aminiya ta ruwaito cewa masunta 15 ne kungiyar ta hallaka a harin da ta kai musu a cikin dare a kauyen Tunbun Rogo da ke Karamar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno, inda wasu da dama suka bace.
A cewar ganau, ’yan ta’addan sun kashe masunta 31, inda iyalai da dama ke jiran labarin uwansu suke.
Gawarwakin wadanda abin ya rutsa da su na ci gaba da zama a cikin daji, yayin da wasu da suka gudu zuwa jejin da ke kusa da su sannu a hankali ke dawowa da raunuka, inda suke ke karbar magani a Cross Kauwa da sojoji ke kula da su.
- Rikicin Sarauta: Alkalan Kano za su gurfana a Abuja kan umarni masu karo da juna
- ’Yan fashi sun duro daga bene ana tsakar tuhumarsu a kotu
- NAJERIYA A YAU: Yadda Dawo Da Tsohon Taken Ƙasa Zai Mayar Da Najeriya Baya
Kamar yadda Aminiya ta ruwaito a baya ’yan ta’addan sun afka wa yankin ne dauke da makamai, suka tare masunta kafin su bude musu wuta.
An kai harin ne bayan da sojoji suka umurci masunta su bar yankin domin gudanar da aikinsu na sintiri da suka saba yi amma kuma ajali ya sa masunta yin biris da umarnin har suka hadu da wadannan ’yan ta’addan suka halaka su.
Wani wanda ya tsallake rijiya da baya a harin ya bayyana cewa, “’Yan ta’adda ne suka taru, suka ce suna son yi mana wa’azi, maimakon haka, kwamandansu ya ba da umarnin a kashe mu.”
A cewarsa, “an kashe akalla masunta 31, kuma sama da 40 daga cikinmu sun yi nasarar tserewa.
“Amma daga baya mun samu labarin cewar, Kwamandan ’yan ta’addan ya hukunta daya daga cikin ’yan ta’addan saboda ya bar wasu daga cikin mu sun gudu.”
Wata majiyar ta tabbatar da cewar, wadanda abin ya shafa masunta ne daga garuruwan Monguno, Doron Baga, Cross Kauwa, da Baga.
Hukumomi ba su ce uffan kan lamarin ba har ya zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto.