Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta bayyana cewa tana fuskantar matsala wajen yakar ’yan ta’adda saboda ɓata-garin da ke bai wa ’yan ta’addan bama-bamai da bayanai.
Wadannan masu kawo kaya da masu ba da labari su ne manyan cikas a Arewa maso Gabas da Arewa maso yammacin kasar nan, a cewar rundunar tsaron.
Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ne ya bayyana hakan a wani taron tsaro da aka gudanar a Abuja.
Christopher Musa ya ce yana da matukar muhimmanci a katse duk abin abin da taimaka wa ayyukan ta’addanci, wanda ya haɗa da dakike dabaru da kudade da ’yan ta’adda ke dogaro da su.
Ya ce a sakamakon katse waɗannan abubuwan a yankin Arewa maso Gabas, kusan ’yan ta’adda 200,000 ne suka miƙa wuya. Janar Musa ya yi imanin cewa yin wannan dabara a faɗin kasar zai kawo sakamako mai kyau.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya kara da cewa taron tattaunawa wani muhimmin dandali ne na tattaunawa a kan nasarori da ƙalubalen da ake fuskanta a fannin tsaro da adalci.