✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nakiyar masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ce ta yi barna a Ibadan —Makinde

Mutum biyu suka rasu, wasu 77 suka jikkata gami da asarar dukiyoyi

Gwamnatin Oyo ta zargi masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da haddasa tashin abin fashewa da ya girgiza birnin Ibadan, inda mutum biyu suka rasu, wasu 77 suka jikkata. 

A yayin da ake ci gaba da aikin ceto, Gwamna Seyi Makinde, ya ce binciken farko ya gano cewa ababen fashewa da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba suka adana a cikin wani gida ne suka  tashi.

“A bisa binciken farko da jami’an tsaro suka gudanar an gano, ababen fashewar wasu masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida da ke zaune a wani gida a unguwar Bodija ne suka. Amma ana ci gaba da bincike kuma duk wanda aka samu da hannu zai fuskanci hukunci,” in ji shi.

Gwamnan ya rubuta ne a shafinsa na X a safiyar Laraba, bayan ya je dubiyar wadanda abin ya shafa a asibitoci, inda ya kara da cewa gwamnatin jihar ta dauki nauyin kudin asibitin duk mutanen da kuma matsuguni ga wadanda suka rasa muhallansu.

An yi asarar dukiyoyi sakamkon feshewar ta daren Talata, wadda karfinta ya jijjiga wurare irin su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan (UHC), Agbowo, Eleyele, Orogun Apete, Eleyele, Onireke, Sango, Agbowo, Mokola, Jericho, Omi Adio da sauransu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wata makarantar kwana na daga cikin wuraren da gobarar ta shafa, kuma an kai wadanda abin ya ritsa da su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan.

Mazauna garin sun bayyana cewa gobarar ta lakume wasu gidaje da wuraren cin abinci da manyan shaguna a birnin na Ibadan; inda gilasan gine gine suka farfashe.

NAN ya bayyana cewa yawan mutanen tsautsayin ya shafa ya tilasta hukumar gudanarwar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan, dawo da ma’aikatanta da ke hutu bakin aiki.

Wani jami’in lafiya a asibitin koyarwan wanda shi ne cibiyar lafiya mafi girma a Jihar Oyo, ya ce, “Akwai bukatar karin ma’aikata domin kula da wadanda ake kawowa, ga shi kuma ba a san yawan wadanda za a iya shigowa da su nan gaba ba.”

Wani abokin aikinsa ya bayyana cewa hukumomin asibitin sun fara tunanin game da yiwuwar kawo mutanen da daga bisani za a kawo su sakamakon tasirin gobarar.

“Ina ganin shirin ba saboda wadanda ake kawowa a halin yanzu ba ne kawai, akwai yiwuwar samun wadanda kaduwa da lamarin zai kawo su, musamman kasancewar abin ya girgiza yankin.

“Masu rauni na zahiri za a iya gane su a halin yanzu, amma akwai masu hawan jini da bugun zuciya da sauransu; wadanda wasunsu sai nan gaban za a gane ainihin halin da suke ciki ko za a kawo su,” in ji shi.

Jami’ar hulda da jama’a na Asibitin, Joke Akinpelu, ta musanta wani labari da ke cewa wani gini ya rushe asibitin a sakamakon tashin abun fashewar.