✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu garkuwa da daliban jami’a mata na neman N50m

’Yan bindiga sun sace dalibai mata biyu mata a Jami'ar Olabisi Onabanjo, da ke Jihar Ogun.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai biyu mata a Jami’ar Olabisi Onabanjo, da ke Ago Iwoye a Jihar Ogun.

Rahotanni sun bayyana cewa daliban mata, an yi garkuwa da su ne a daren ranar Lahadi a Karamar Hukumar Yewa ta Arewa.

Aminiya ta gano yadda ’yan bindigar suka yi shigar burtu sannan suka sace daliban.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu, cewar ‘yan bindigar sun tuntubi iyalan daliban, inda suka bukaci Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa.

Kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.

Amma ya ce hadin gwiwar jami’an tsaro sun baza koma don kubutar da su daga hannun wanda suka yi garkuwa da su.