’Yan bindigar da suka sace tsohon Kansilan gundumar Gurdi da ke karamar hukumar Abaji a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja, sun sako shi tare da ba shi babur don ya tara musu Naira miliyan takwas.
Masu garkuwar dai sun saki Mohammed Ibrahim Tanko, wanda suka kama ranar Lahadi ne sannan suka ba shi babur din domin ya samu ya tara musu kudin, kafi su saki sauran mutanen da suka kama tare da shi.
- Zan bayar da tallafin N7trn a kwana 100 na farkon mulkina muddin aka zabe ni – Atiku
- Saudiyya ta tsare mutumin da ya yi wa Sarauniya Elizabeth II Umarah
Aminiya ta rawaito yadda maharan suka farmaki garin Tekpeshe da ke yankin, inda suka kashe mutum daya suka kuma sace wasu 18, cikinsu har da tsohon Kansilan.
Wani mazaunin Tekpeshe, Yakubu Ibrahim, ya shaida mana ta wayar salula cewa ’yan bindigar sun saki Mohammed ne tare da wasu mutum hudu da yammacin Litinin.
Ya ce, “Gaskiya ne an saki tsohon Kansilanmu tare da wasu mutum hudu da yammacin Litinin. Sun kuma ba shi babur domin ya je ya tara musu Naira miliyan takwas da kayan abinci, sannan ya kai musu kafin su saki ragowar wadanda suka kama tare da shi.”
Ya kuma ce tuni tsohon Kansilan ya fara tuntubar iyalan wadanda har yanzu suke tsaren don ganin yadda za a samu a tara kudaden da suka bukata.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Abuja, DSP Daniel Josephine ba ta amsa rubutaccen sakon kar-ta-kwanan da wakilinmu ya aika mata da shi ba a akan lamarin.