’Yan bindigar da suka yi garkuwa da mutum biyar ’yan gida daya a Unguwar Sauri a Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna na neman a ba su Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa.
Rahotanni sun ce ’yan bindiga sun shiga yankin ne suka yi garkuwa da Peter Andrew Umoh da matarsa da kuma ’ya’yansu uku.
- Hukumomin gwamnati sun gana a kan laifukan intanet
- Majalisar Kano ta ba Ganduje awa 48 ya kori shugaban hukumar haraji
Sai dai ’yan bindigar sun kyale mahaifiyar magidancin mai shekara 86 a duniya, saboda ganin ta tsufa.
Dattijuwar ta bayyana cewa a danginta gaba daya babu wanda yake da Naira miliyan 20 da ’yan bindigar suke nema.
“Ina rokon ’yan Najeriya da su taimaka min a ceto ’ya’yana da jikoki,” a cewarta.
Misis Josephine Andrew, kanwa ga Peter, wanda ’yan bindiga suka yi awon gaba da shi da iyalansa, ta bayyana cewa ’yan bindigar sun ki karbar tayin N300,000 da iyalan suka ce yi musu.
Ta ce suna cikin fargaba kada ’yan bindigar su hallaka musu ’yan uwa, don haka tana neman taimakon ’yan Najeriya.
A jihar Kaduna dai gwamnati ta hana ba wa ’yan bindiga kudin fansa a fadin jihar.