Masu ta’adar garkuwa da mutane sun yi awon gaba wasu yara shida da suka kasance ’ya’yan wani Alhaji Sani Gyare a kauyen Kadauri da ke Karamar Hukumar Maru a jihar Zamfara.
Rundunar ’yan sandan jihar ce ta tabbatar da faruwar lamarin yayin da mai Mai Magana da yawunta, SP Shehu Muhammad ya zanta da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN.
- Ganduje zai ba Kwankwaso sarautar mahaifinsa
- Ko Arewa24 sun nemi in dawo Kwana Casa’in ba zan dawo ba –Safara’u
- Tsohon Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda Tambari Yabo ya rasu
SP Shehu ya ce, sun tabbatar masu garkuwar sun yi awon gaba da yara bakwai a kauyen na Kadauri, shida a gidan Alhaji Gyare sai kuma yarinya daya a gidan wani makwabcinsa.
Ya ce, “Kwamishinan ’yan sanda CP Abutu Yaro ya tura runduna ta musamman domin a ceto yaran.”
“Kwamishinan wanda ya ce an samu zaman lafiya a yanki, ya sha alwasin ceto wadanda lamarin ya ritsa da su nan ba da jimawa ba.
“Ya bukaci mazauna yankunan da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanai da za su taimaka wajen dakile aukuwar makamanciyar wannan mummunar ta’ada,” inji SP Shehu.
Rahoto ya bayyana cewa masu garkuwar sun kai hari kauyen ne a ranar Juma’a da daddare inda suka ci karensu babu babbaka sannan suka kama gabansu.
Mahaifin yaran shida ya ce yana zargin sammatsin da ya yi da maharani ya sanya suka yi awon gaba da yaran a maimakonsa.
“An sanar da ni cewa lokacin da suka isa kauyen, kai tsaye suka tafi gidana.”
“Bayan sun fahimci cewa bana gida, sai suka tafi da ’ya’yana da kuma diyar wani amini na kuma makwabcina, Alhaji Sani Yellow,” inji shi.