✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rigima ta sake kaurewa tsakanin PDP da APC a Zamfara

APC ta ce za ta soma ɗaukar mataki kan duk wani da ya yi yunƙurin cin zarafin mambobinta.

Wani sabon rikici ya sake kunno kai a tsakanin manyan jam’iyyun siyasa biyu a Jihar Zamfara.

Rigimar wadda ta kunno tsakanin APC da PDP ta samo asali ne tun bayan da wasu matasa suka yi yunƙurin hana wani taro na ɗan Majalisar Wakilai da za a gudanar a garin Maru.

Hakan ya sa Gwamnatin Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ta ɗauki wani matakin da take ganin zai kawo lafawar lamarin.

Sai dai kuma matakin da gwamnatin ta ɗauka bai yi wa jam’iyyar APC daɗi ba, inda ta nuna rashin gamsuwa tare da zargin ba a yi mata adalci ba saboda kasancewarta jam’iyyar adawa.

A bayan nan ne Gwamnatin Zamfara ta dakatar da duk wasu tarukan siyasa a jihar saboda samar da zaman lafiya da daidaito.

A bayanin da mai taimaka wa Gwamnan Zamfara kan kafafen yaɗa labarai, Mustapha Jafaru Kaura ya fitar, ya ce matakin na zuwa ne bayan hatsaniyar da aka samu a tsakanin jam’iyyun PDP da APC a Ƙaramar Hukumar Maru.

“Duk wani taron siyasa da zagaye an dakatar da shi a wannan lokaci, la’akari da abin da ya faru a Maru inda aka samu salwantar rayuka da ƙone-ƙonen dukiya.”

Hadimin gwamnan ya ce an ɗauki matakin ne ba don a musguna wa wasu ba face sai don samar da zaman lafiya kuma dokar da aka sanya ta wucin gadi ce.

Jam’iyyar APC a Zamfara ta nuna rashin gamsuwar ta kan matsayar da gwamnatin ta ɗauka tana mai zargin cewa gwamnatin ta mayar da hankali kan abin da ba shi ne ya fi ba.

Wata sanarwa da APC ta fitar ta bayyana cewa dole ne hukumar ’yan sanda a jiha ta kama waɗanda suka kai farmaki ga magoya bayanta a yayin da suke gudanar da kowane taro.

Jam’iyyar ta ce gargaɗin ya zama wajibi ganin yadda ‘yan sanda suka fita batun koken da aka gabatar musu a rubuce har guda uku.

“A cikin matasan da muke zargi, ’yan bangar siyasa daga jam’iyyar PDP da ’yan sa kai ne suka kawo farmaki a wurin rabon kayan ɗan Majalisar Wakilai na Maru da Bungudu, Honarabul Abdulmalik Zubairu Bungudu.

“Ɓatagarin sun laɓe ne kan hanyar Gusau zuwa Bungudu inda suka kai harin kan magoya bayan APC sannan suka lalata ababe hawa da dama.

Sakataren yaɗa labarai na APC a Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya yi tir da lamarin, yana mai kiran jami’an tsaro su ɗauki matakin gaggawa.

Idris Gusau ya ce “muddin ba haka ba zai sa mu riƙa kare kansu kan kowane mutum da ya nemi cin zarafinsu.”

Sakataren ya nemi magoya bayansu da su kwantar da hankali domin za a tabbatar da an yi adalci ga waɗanda aka ji wa rauni ko aka ɓarnata dukiyoyinsu.

“A matsayinmu na masu son zaman lafiyar Jihar Zamfara ba za mu bari a yi amfani da mu don kawo hargitsi ba kamar yadda jam’iyyar PDP ke kitsawa,” in ji shi.