Aminiya ta gano cewa ’yan bindiga wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ranar Litinin sun kashe wani dan sanda kuma suka sace dan kasar Jamus wanda inginiya ne da ke aiki da kamfanin gine-gine na Dantata da Sawoe mai suna Mista Michael Cremza a jihar Kano.
Lamarin ya auku ne dab da gadar Madobi da misalin karfe bakwai da minti 45 na ranar yayin da dan kasar Jamus din da dan sandan da ke kare lafiyarsa suke kan hanyarsu ta zuwa wurin aikin da kamfanin yake yi a yankin.
Yayin da yake tabbatar da lamarin, Mai Magana Da Yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Magaji Musa Majiya ya ce ’yan bindiga biyar ne suka sace dan kasar Jamus din.
Majiya ya ce “’Yan bindiga a cikin wata karamar mota wadanda suka yi wa motar da ke dauke da Mista Cremza da dan sandan da ke kare lafiyarsa kwantan bauna, suka bude musu wuta inda suka kashe dan sandan da ke kare lafiyarsa mai mukamin saja wanda ke aiki da rundunar ta musamman mai bayar da kariya sannan kuma suka sace dan kasar Jamus din”.