Rundunar ’yan sanda a Jihar Gombe ta cika hannunta da wasu mutum hudu da ake zargi sun addabi garuruwan Kashere da Pindiga na Karamar Hukumar Akko ta Jihar da ta’adar garkuwa da mutane.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, sashin ’yan sandan sintiri ne ka da alhakin cafke ababen zargin a maboyarsu da ke Dajin Gobirawa wadanda rahotanni sun bayyana cewa sun addabi Kudancin Gombe da wasu yankuna na jihar Bauchi da Taraba da ke makwabtaka da jihar.
- Romania za ta karbi daliban Najeriya daga Ukraine su karasa karatunsu
- Buhari ya tafi Landan ganin Likita
’Yan sanda sun kama ababen zargin hudu ne a wani shingen binciken ababen hawa da suka kafa, inda binciken ya gano cewa masu garkuwa da mutane ne da ke karbar kudin fansa a tsakanin Dajin na Gobirawa da ya yi iyaka da jihohin uku.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a gaban manema labarai, Kwamishinan ’yan sandan Jihar Gombe, Ishola Babatunde Babaita, ya ce mutanen sun bayyana cewa su ne suka yi garkuwa da wani da ake kira Yellow dan asalin jihar Taraba da suka karbi kudin fansa naira dubu dari biyar sannan suka sake shi.
Bayan bayyana wa manema labarai sunayensu da kuma shekarunsu na haihuwa, Kwamishinan ’yan sanda ya ce da zarar sun kammala bincike za a gurfanar da su a gaban Kuliya domin su girbi abin da suka aikata.
Bayanai sun ce daga cikin makaman da aka samu a hannun ababen zargin sun hada da bindiga kirar AK 47, da wadansu bindigogin kirar gida da harsasai masu yawa da kuma adduna guda biyu.
A wani labarin mai nasaba da wannan da Aminiya ta ruwaito, ’yan sandan sun cafke wani mutum da ake zargi mai garkuwa da mutane ne mai suna Adamu Umaru dan shekara 28 a kauyen Garbabi da ke Jihar Taraba.
An samu nasarar cafke wannan matashi a sakamakon bayanan sirri da jami’an ’yan sandan yankin Gona na Karamar Hukumar Akko ta Jihar Gombe suka samu.
Rahotanni sun ce wannan matashi dai yana tara yara yake koya musu yadda za su yi garkuwa da mutane don neman kudin fansa a Jihar Taraba.
Kwamishinan ’yan sandan Ishola Babaita, ya ce daya daga cikin yaran nasa ne ya sanar da mahaifinsa kan wannan shiri, inda ta nan ne asirin sa ya tonu kuma wanda ake zargin ya amsa laifinsa da cewa ya kitsa garkuwa da mutane da dama wanda kuma ya yi nasara.
Babaita ya ce da zarar an kammala bincike za a tura shi zuwa kotu.