Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da basaraken yankin Masarautar Uwano Kingdom, Dakta George Oshiapi Egabor, nan take saboda matsalar yi garkuwa da mutane a yankin.
Dakta George Oshiapi Egabor shi ne Okumagbe na Masarautar Uwano da ke Agenebode a Karamar Hukumar Etsako ta jihar.
Kakakin gwamnan, Fred Itua, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa an dakatar da basaraken ne har sai abin da hali ya yi, saboda yawan samun kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane a masarautarsa a baya-bayan nan.
Ya ce tuni jami’an tsaro suka tsare sakataren basaraken, Cif Peter Omiogbemhi, sakamakon wani sabon hari a da ya yi ajalin wani bafade, Cif John Ikhamate.
- Mutanen da aka kashe a Binuwai sun ƙaru zuwa 72
- An tsinci gawar saurayi da buduwarsa a tuɓe a cikin daƙi
A baya-bayan nan an samu yawaitar garkuwa da mutane a yankin, wanda ya haddasa ƙone ofishin ’yan sandan da ke kula da yankin.
Daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su har da wasu malaman coci guda uku da aka yi aka yi awon gaba da su a wani coci, inda daga baya aka sako biyu bayan an biya kudin fansa, na ukun kuma aka kashe.