Rundunar ’yan sanda a Jihar Taraba ta cafke mutane tara kan zargin satar mutane.
Haka kuma, rundunar ta gano bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu da kuma bindigogi ƙirar AK-49 guda uku da alburusai guda arba’in da biyar a hannun waɗanda aka cafke.
- Dalilin faɗuwar farashin kayan abinci a kasuwannin Arewa
- Ƙungiyoyin da suka yi shuhura a Firimiyar Ingila
Kakakin rundunar ’yan sandan, ASP James Lashen ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a birnin Jalingo.
Ya bayyana sunayen ababen zargin da aka kama da suka haɗa da Shehu Ibrahim da Abdullahi Haruna da kuma Yusuf Bello.
Sauran kuma sun haɗa da Sulaiman Muhammed da Tijjani Bello da Muhammed Umar.
Kazalika, akwai kuma Adamu Ibrahim da Solomon Nathaniel da kuma Haruna Adamu.
ASP James, ya ce ’yan sanda sun sami nasarar kama waɗanda ake zargin ne bayan samu bayanan asiri dangane da ayyukansu.
Ya ce waɗanda aka kama sun shaida wa ’yan sanda cewa suna daga cikin guggun masu satar mutane a jihohin Gombe da Filato da Kaduna da Bauchi da kuma Jihar Taraba.
ASP James ya bayyana cewa ana ci gaba da faɗaɗa bincike kan ababen zargin kuma nan gaba kaɗan za a gurfanar da su a kotu.
Ya ce kwamishinan ’yan sanda, Emmanuel Bretet ya ɗauki alwashin murkushe masu aikata laifuka a Jihar Taraba domin ganin an kare rayuka da dukiyar al’umma.