Wadanda suka yi garkuwa da tsohon Daraktan Lafiya kuma mamallakin asibitin Aisha, Dokta Saidu Bala sun nemi iyalinsa tare da bukatar makudan kudade don fansarsa.
’Yar uwar Dokta Saidu, wadda kuma rajistara ce a Jami’ar Modibbo Adama (MAU) da ke Yola, Halima Bala ta tabbatar da lamarin.
- ’Yan gudun hijirar Afghanistan 6 sun mutu a hatsarin mota a Iran
- Najeriya A Yau: ‘Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Katobara Kan Matsalar Tsaro’
“Sun kira mu da safiyar nan kuma mun yi magana da dan uwana, ya tabbatar min yana cikin koshin lafiya.
“Dan uwana ya ce mu nemo kudin fansar, shi ne kadai abin da ya ce da ni mu nemo kudade masu tarin yawa,” a cewarta.
Dokta Saidu dai an sace shi ne a ranar Litinin yayin da ya ke tsaka da duba mara lafiya a asibitinsa da ke unguwar Ngurore a garin Yola.
“Tabbas, mutum uku zuwa hudu dauke da bindigoagi sun shiga asibitin bayan Sallar Magariba sannan suka dinga harbi wanda hakan ya sa mutane tserewa,” inji Halima.
Kakakin ’yan sandan jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, ya bada umarnin ceto likitan cikin koshin lafiya.
“Kwamishinan ya bayar da tabbaci ga iyalan Bala cewar za a tseratar da shi cikin koshin lafiya,” a cewarsa.