An gurfanar da wasu masu gadi su biyu a wata kotun Majistare a Jihar Legas bisa zargin satar sarrafaffen kanzon kwali da aka fi sani da ‘Corn Flakes’ a Turance, har katan 400 wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 2.1.
’Yan sanda sun gurfanar da masu gadin, Monday Ulelu da Mubarao Azeez ne bisa zargin hadin baki da kuma yin sata.
- Maniyyatan Kano sun yi zanga-zangar rashin samun tafiya Saudiyya
- An tsinci gawar mutum 46 da ke son tsallakawa Amurka ci-rani daga Mexico
Su biyun sun ki amsa aikata laifin da aka tuhume su da shi a gaban kotu.
Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Benedict Aigbokhan, ya shaida wa kotun cewa masu gadin sun sun saci katan 400 na ‘Nabeu corn flakes’ wanda kudinsu ya kai miliyan N2.1, mallakar wata mai suna Misis Bintu Osifodumn.
Ya kara da cewa, wadanda ake zargin suna aikin gadi ne a gidan da aka adana kayan, a ranar 13 ga Yuni, a yankin Ikotun, a birnin Legas kuma suka kasa ba da kwakkwaran bayani kan yadda aka yi kayan suka bace.
A cewarsa, wannan laifi ne da ya saba wa Sashe na 287 da na 411 na Kundin Dokokin Jihar Legas na 2015.
Daga bisani alkalin koton, K. A. Ariyo ta ba da belin wadanda ake zargin kan N500,000 kowannensu tare da gabatar da shaidu guda biyu-biyu.
Ta kuma shardanta cewa tilas shaidun su kasance ma’aikata, su kuma nuna shaidar biyan haraji ga Gwamnatin Jihar Legas.
Daga nan, ta dage ci gaba da sauraren karar zuwa 28 ga Agusta, 2022.