Hukumar tsaro ta NSCDC shiyyar Kaduna ta ce ta kama mutum 19 bisa zargin aikata fyade a jihar tsakanin watan Agusta da Satumba.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dokokin jihar ta yi dokar dandake masu fyade wadda Gwamna Nasir El-Rufai ya rattaba wa hannu.
- El-rufa’i ya sa hannu kan dokar dandake masu fyade a Kaduna
- Tsoho mai shekara 60 ya yi wa ‘yar cikinsa fyade
Kakakin Rundunar, ASC Orndiir Terzungwe shine ya bayyana hakan yayin da yake yi wa ‘yan jarida jawabi a hedikwatar rundunar da ke Kaduna ranar Juma’a.
Ya ce ana zargin mafi yawan wadanda aka kama ne da lalata yara kanana.
Orndiir ya ce, “A kokarinmu na rage yi wa yara kanana fyade, NSCDC a Jihar Kaduna ta samu nasarar cafke akalla mutum 19 daga watan Agusta zuwa yau.
“Idan an lura sosai za a fahimci cewa rundunarmu na neman tallafin jama’a a koyaushe, kuma muna godiya da yadda suke ba mu tallafi.
“Sai dai abin takaicin shi ne kusan dukkannin wadanda lamarin ya shafa kananan yara ne”, inji shi.
Ya ce wasu daga cikin yaran sun kamu da cututtuka, kuma an gurfanar da 18 daga cikinsu wadanda ake zargin a gaban kuliya tare da kwarin gwiwar cewa kotun za ta aike da su gidan kaso.
“Abin takaici ne matuka yadda ake samun wannan matsalar duk da irin tsauraran dokokin da Gwamnatin Jihar Kaduna ke yi kan masu aikata laifin.
“Za mu ci gaba da yin duk abin da yake a bisa doron doka wajen ganin mun magance hakan,” inji shi..