’Yan bindigan da suka sace Fasto Samson Ndah Ali na cocin ECWA da ke Mararaba Aboro a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, sun sake shi sannan sun tsare wanda ya kai kuɗin fansar, Yusuf Shehu Ambi, wanda shi ne sakataren cocin.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, dattijon da ke matsayin jami’in koci na cocin ne ya kai kuɗin fansar, inda ’yan bindigar suka ƙi sakinsa bayan sun karɓi kuɗin.
- Sanƙarau: An tabbatar da ɓullar cutar ga mutane 300 a Sokoto
- ’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi
“An saki faston, amma suka ci gaba da tsare mutumin da ya kai musu kuɗin. Ba mu san dalili ba, muna cikin fargaba da alhini,” in ji majiyar.
An sace Fasto Ali, mai shekara 30, daga gidansa da misalin ƙarfe 1 na dare a ranar 8 ga Afrilu, ƙasa da makonni biyu da naɗa shi zuwa cocin.
Tun da farko, masu garkuwar sun buƙaci kuɗin fansa Naira miliyan ɗari (N100m) ne daga shugabannin cocin.
Ƙoƙarin Aminiya na jin ta bakin hukumomin tsaro bai ci nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.