✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu fataucin miyagun kwayoyi ba mutane ba ne – Shugaban Philippines

Shugaban kasar Philippine Mista Rodrigo Duterte, wanda ya kaddamar da yaki kan aikata miyagun ayyuka a kasarsa, ya kare kashe masu fataucin miyagun kwayoyi da…

Shugaban kasar Philippine Mista Rodrigo Duterte, wanda ya kaddamar da yaki kan aikata miyagun ayyuka a kasarsa, ya kare kashe masu fataucin miyagun kwayoyi da gwamnatinsa ke yi, inda ya bayyana su da cewa ba mutane ba ne.
Kamfanin Dallancin Labarai na AFP, ya ruwaito cewa Shugaba Duterte, wanda aka kashe mutum dubu biyu bayan zabensa a watan Mayun bana, ya bayyana haka ne a ranar Juma’ar da ta gabata, lamarin da ke nuna watsi ne da korafin Majalisar dinikin Duniya kan keta hakkin dan Adama a kasarsa.
Ya shaida wa sojoji lokacin da ya ziyarci wani sansanin soji cewa: “Cin zarafin dan Adam? Da farko zan gaya muku gaskiya: Shin su mutane ne? Me za ku fassara dan Adam?”
“Hakkin dan Adam? Yi amfani da kalmar yadda ta kamata idan kana da kwakwalwa,” ya sake cewa.
Shugaba Duterte ya kara da cewa: “Ba za ka kaddamar da yaki ba, ba tare da kisa ba,” inda ya ce masu fataucin miyagun kwayoyi da dama ba za su taba tuba ba.
Jawabin nasa ya zo ne bayan da jami’an Majalisar dinkin Duniya da dama ciki har da Babban Sakataren Majalisar, Mista Ban Ki-Moon wadanda a watan Yuni suka soki yadda Shugaban yake goyon bayan kisan mutanen da ake zargi ba tare da yi musu shari’a ba.
Bayanin Duterte ya kuma zo ne a lokacin da shugaban ’yan sandan kasar Ronald Dela Rosa a ranar Juma’ar ya buaci mashaya miyagun kwayoyin su rika kashe masu fataucin miyagun kwayoyin suna kone gidajensu.
Dela Rosa ya ce: “Me zai sa ba za ku kai musu ziyara ku watsa fetur a gidajensu ku sanya musu wuta ba, domin ku nuna musu bacin ranku?”
Daga baya Dela Rosa ya nemi afuwa kan kalaman nasa. Amma Shugaba Duterte ya kare shi ta hanyar cewa: “wannan ne salona. Yana bi salona ne.” Shugaba Duterte ya yi gatse ga Majalisar dinkin Duniya cewa: “suna son a kai ni kurkuku ne? Wadannan mutanen banza suna tunanin za a kama ni da raina ne. Ina sai dai mu hadu a Lahira.” A farkon wannan mako, Dela Rosa ya shaida wa sanatocin kasar cewa ’yan sanda sun kashe kimanin mutum 750 a yakin da suke yi da masu fataucin miyagun kwayoyi, yayin da dubbai suka mutu saboda ayyukan masu fataucin miyagun kwayoyin.Shugaba Duterte mai shekara 71, ya lashe zaben watan Mayu ne tare da gagarumar rinjaye sakamakon alkawuran day a rika yin a kashe dubban wadanda ake zargi da aikata miyagun ayyuka domin hana kasar Philippines kasancewa kasar masu tu’ammali da miyagun kwayoyi. Kuma ya yi alkawarin kare ’yan sandan da za a iya tuhuma saboda daukar wannan mataki.