Masu ba da tallafi sun yi alkawarin bayar da tallafin kimanin Dala miliyan 700 don magance matsalolin jin kai a yankin Tekun Chadi, inda Najeriya za ta samu kaso mafi tsoka daga tallafin da za a ba yankin.
Bayanin haka na kunshe ne a cikin kalaman da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Mista Geoffrey Onyeama a ranar Talatar da ta gabata a Abuja, yayin ganawar sirri da ya yi da ayarin Majalisar dinkin Duniya (UN) a karkashin jagorancin karamin Sakataren Harkokin Jin kai kuma Kodinetan Ayyukan Jin kai na majalisar, Mista Mark Lowcock.
Idan za a iya tunawa a watan Fabrairun bana Majalisar dinkin Duniya ta shirya taron neman gudunmawar Dala biliyan 1.5 daga masu ba da tallafi a birnin Oslo na kasar Norway don magance matsalolin da ke addabar yankin na Tekun Chadi.
Masu ba da tallafi sun yi alkawarin karin fiye da Dala miliyan 670, a wurin taron a kasar Norway da hadin gwiwar Najeriya da Jamus suka dauki nauyi, don karfafa ayyukan tallafi a yankin. Ministan ya jinjina wa Majalisar dinkin Duniya bisa rawar da ta taka wajen shirya taron, sai dai ya ce akwai kalubale masu yawa wajen cika alkawuram na masu bayar da tallafi. Kuma ya ce, ayyukan suna samun ci gaban da ke nuni da nasararsa.
Tun farko Mista Lowcock ya bayyana cewa yana Najeriya ne domin gani da ido kan matsalar ayyukan jin kan dan Adam a Arewa maso Gabas kuma zai mika rahotonsa ga Babban Taron Majalisar dinkin Duniya. “Zirayata domin in gani da ido ne game da halin da ake ciki a nan, kuma a gefe guda in fahimci ci gaban da aka samu a harkokin rayuwar jama’a da suke neman tallafin jin kai,” inji shi.
Mista Lowcock ya ce zai je yankin Arewa maso Gabas ganawa da mutanen da lamarin ya shafa da kuma abokan hadin gwiwa a ayyukan jin kai don auna yadda ake tallafa musu.
Jami’in na Majalisar dinkin Duniya, ya kuma bayyana cewa ziyarar za ta ba shi damar ganawa da jami’an gwamnati a Arewa maso Gabas, tare da neman a kara yawan tallafin da ake bayarwa ga garuruwan da lamarin ya shafa.
Mista Lowcock ya ce ziyarar tasa har ila yau za ta kara janyo hankalin duniya kan yankin da kuma abin da ya shafe shi, inda ya ce tallafin za a mayar da hankali a kan mata da yara, saboda karuwar damuwar da ake da ita kan ba su kariya da samar musu da abinci da tabarbarewar harkokin lafiyarsu kamar yadda aka samu barkewar cutar amai da gudawa a sansanonin ’yan gudun hijirar a baya-bayan nan.