Wasu mata masu aikin shara su 11 a kasar Indiya, sun lashe Dalar Amurka miliyan 1.2, kwatankwacin sama da Naira tiriliyan daya a wata caca.
Matan sun lashe cacar ce da kudin suka kai Rupee miliyan 100 a kudin kasar ta Indiya a watan Yunin da ya gabata, a wajen aikinsu da ke Parappanangadi a birnin Malappuram da ke kasar.
A cewar daya daga cikin matan mai suna M Radha, lokacin da ta duba wayar salularta ta ga sakon da ke cewa sun lashe gasar a ranar 27 ga watan Yuli, sun cika da matukar farin ciki.
Ta ce, “A nan take na barke da ihu sannan na rungume abokan aikina da muka lashe tare.
“Ba mu taba shiga farin ciki irin wannan ba a rayuwarmu. A baya mun sha sayen tikitin cacar, amma lokacinmu na lashe ta bai yi ba sai yanzu,” in ji ta.
Matan dai na aikin gyara shara ne domin cire abubuwan amfani daga cikinta a wani kamfani da ke birnin Parappanangadi.
Sun ce kafin su ci wannan gasar, sukan yi rayuwar hannu baka hannu kwarya ne, kuma abin da suke samu bai wuce Naira 4,000 ba a wuni.
Ta ce hatta lokacin da aka tallata musu cacar a watan Yuni, ba su da Rupee 250 kudin tikitin shigarta, sai da suka hadu su 10 suka yi karo-karo kafin su hada Rupee 250.
Radha ta kuma ce daya daga cikinsu ma ba ta iya kawo nata Rupee 25 din ba, sai da ta haɗa gwiwa da wata ’yar uwarsa, dalili ke nan ma da yawansu sai da ya kai su 11.