Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya yi kira ga jami’an kashe gobara da sauran masu ruwa da tsaki da su binciki musabbabin tashin gobarar da aka samu a wasu sassa na Majalisar Dokokin Jahar a safiyar Laraba.
Gwamnan yayi wannan kira ne a lokacin da dan majalisa mai wakiltar mazabar Kankiya, Hon. Suleiman Hamza Rimaye ya zagaya shi wuraren da gobarar ta tashi.
- Buhari ya sake nada Jelani Aliyu a matsayin shugaban NADDC
- Shin da gaske an haramta yin tashe a Kano?
Gobarar dai wacce har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a san musabbabinta ba, ta yi mummunar barna, cikin Majalisar, ciki har da harabarta.
A cewar wani ganau, babu wanda ya san daga inda wutar ta faro balle dalilin ta shin ta.
Babu dai wani rahoton rasa rai ko jikkatar wani sanadiyar wannan gobara ya zuwa yanzu.
Idan za a iya runaway, a kwanakin baya an samu tashin irin wannan gobarar a babbar kasuwar Katsina inda aka yi asarar dukiya ta milyoyin Nairori.