✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun yi garkuwa da fiye da mutum 50 a Katsina

’Yan bindigar sun kuma kashe aƙalla mutum takwas bayan da suka shafe sama da awa 24 suna cin karensu babu babbaka a ƙauyukan ƙananan hukumomin…

Mazauna yankin ƙaramar hukumar Funtua ta Jihar Katsina sun ce ’yan bindiga sun shiga wasu ƙauyukan yankin, inda suka kwashi mutane sama da 50 da suka hada da mata da ƙananan yara.

Maharan sun kuma kashe akalla mutum shida, inda suka sake kai wani hari a yankin Ƙaramar Hukumar Ɗandume ta jihar.

Rahotanni sun ce tun daga ranar Asabar maharan suka shiga yankin kuma ba su fita ba har zuwa ranar Lahadi da rana.

Malam Ya’u Ciɓauna mazaunin garin Layin Gara ne na Ƙaramar Hukumar Funtua, kuma ya ce “Misalin 10:30 na dare suka zo kuma sun kwashi maza da mata da ’yan mata da matan aure da kuma ƙananan yara har 53.

“Sun kashe mutum a Layin Gara na Ƙaramar Hukumar Funtua da kuma wasu mutum biyu a garin Mai Kwama a cikin Karamar Hukumar Ɗandume,” in ji Malam Ya’u.

Shi ma maigarin Layin Gara, Mustapha Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa mutanensa na cikin mawuyacin hali na rashin abinci, kwatsam kuma sai ga wannan matsala ta harin ’yan bindiga.

“Gwamnati tana ji tana gani wani abin ba a yi mana. Sojoji ma yadda ake turowa mu ba mu samu gatan an turo mana su ba, ’yan sandan da suka zo sai dai suka wuce suka nufi gardawa,” in ji Mustapha Abdullahi.

Matsalar tsaron dai ta tilasta wa mutanen yankin yin hijira da ɗan sauran abubuwan da suka rage masu, kamar yadda mai garin Layin Gara ke cewa.

Hukumar ’yan sanda a jihar ta Katsina dai ta ce tana kan bincike a kai lamarin, domin haka ba za ta ce komai ba sai ta kammala.

Matsalar tsaro na ci gaba da zama ƙarfen ƙafa a Jihar Katsina, kuma yayin da al’ummar da abin ya shafa ke ƙorafi da neman hukumomi su tashi tsaye wajen ba su kariya, gwamnati da sauran jami’an tsaro na cewa suna bakin ƙoƙarinsu wajen magance matsalar.