Karon farko tun bayan zamowarsa shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai ziyarci Jihar Katsina.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Zango, ne ya shaida wa manema labarai hakan a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce shugaban zai kai ziyarar ce, domin ƙaddamarwa da kuma rangadin wasu ayyukan da Gwamna Umar Dikko Radda ya aiwatar a jihar.
- Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya
- Yadda ’yan Tifa da baƙin direbobi ke haddasa haɗari a Abuja
Karin bayani na tafe.