Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce wajibi ne shugabannin Kananan Hukumomin Jihar su tashi tsaye wajen yaki da ’yan bindigar da suka addabi yankunansu, ba tare da jiran wani ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani taro su tare da Kansilolinsu kan sha’anin tsaron Jihar.
- Yan bindiga sun sace matar soja da wasu mutum 6 a Kaduna
- Likitoci sun cire idon mara lafiya ‘bisa kuskure’ yayin tiyata
Offishin mai bai wa Gwamna Shawara kan haekokin tsaro karkashin Alhaji Ibrahim Muhammad Katsina ne ya shirya taron domin duba matsalar tsaron da ta addabi Jihar.
A cewar Masari, wajibi ne su fito su kare tare da ceto yankunan nasu ba tare zaman jiran sai an nemo su ko an kawo masu dauki daga wani waje ba.
Ya ce, “Lallai ku sance tare da jama’arku a kowane lokaci, ba cewa naje Kano, Kaduna ko Abuja ba.
“Domin shi mulki ba abin ado ba ne, abu ne mai tattare da kalubale iri-iri. Saboda, zamanku cikin al’ummarku shi yafi komai muhimmaci domin hidimomin jama’ar aka zabe ku.
“Wajibinku ne ku tsaya don ganin kun ceci al’ummar da kuke mulka daga hare-haren ‘yan ta’addan nan, ku kai dauki a duk inda aka neme ku”, kamar yadda Gwamnan ya ce a wajen taron.