Ganin irin yadda matasa suka yi nisa wajen tara gashi da yin askin da bai dace ba, da kuma sanya matsatsun wanduna da riguna a masarautar Saminaka da ke Jihar Kaduna. Masarautar ta dauki matakin sanya dokar hana aikata wadannan abubuwa a dukkan fadin masarautar.
Masarautar ta dauki wannan mataki ne bayan da ta yi taro da shugabanni al’umma da shugabanni addini na masarautar sakamakon koke-koken da jama’ar masarautar suke ta yi kan wannan al’amari.
Tuni wannan doka ta fara aiki a masarautar, inda wasu matasa suka fito don bayar da gudunmawarsu wajen aiwatar da wannan doka ta hanyar yi wa duk matashin da suka samu ya tara gashi aski. Har’ila yau duk matashin da suka kama ya sanya matsatstsan wando ko matsatsiyar riga suna yagawa.
Da yake zantawa da jaridar Aminiya kan wannan doka da masarautar ta kafa, Mai martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani ya bayyana cewa masarautar ta kafa wannan doka ne saboda koke-koken jama’ar masarautar kan wannan matsala.
Ya ce don haka masarautar ta yi zama da shugabannin yankin ta tattauna da su daga nan ta dauki wannan mataki.
‘’Wadannan yara namu askin da suke yi, aski ne irin na masu miyagun halaye na waje. Kuma suna ganin irin wadannan miyagun mutane ne a tashoshin tilibajin na waje. Ganin yadda wannan abu yake ta ci gaba, yasa jama’ar wannan masarauta suka bukaci a dauki mataki na sanya doka kan wannan mummunan abu,” Inji sarki.
Sarkin ya yi bayanin cewa matasan wannan masarauta ne suka ce za su gudanar da wannan aiki, don su bada gudunmawarsu wajen magance wannan al’amari.
Ya ce a kowace unguwa an shirya matasa wadanda za su bi duk yaran da suka tara gashi su yi masu aski ko kuma su kama duk matashin da ya sanya matsatstsan wando su yaga.
Ya kara da cewa daga lokacin da aka fara aiwatar da wannan doka zuwa yanzu an sami gagarumar nasara. Duk da cewa ana samun tirjiya daga wasu matasan masu irin wadannan halaye.
Kuma ya ce sun bai wa yaran da suke gudanar da wannan aiki dama su mika duk yaron da ya yi masu tirjiya zuwa ga ‘yan sanda domin a kai shi gaban kotu.
A zantawar da jaridar Aminiya ta yi da wasu iyayen yara na wannan masarauta, kan wannan al’amari sun nuna matukar farin cikin su da daukar wannan mataki na kafa wannan doka a masarautar.
To amma wasu matasan da jaridar Aminiya ta tattauna da su kan wannan doka da aka kafa a wannan masarauta sun nuna bacin ransu. Suka ce akwai laifuffuka da dama da ake aikatawa wadanda suka fi wadannan abubuwa da suka kamata a dauki mataki na hana su.