✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masarautar Jama’a ta tube rawanin Sarkin Yaki da Sarkin Fada

Majalisar Masarautar Jama’a da ke Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna ta tube rawanin Sarkin Fadan Jama’a, Alhaji Abdullahi Zubairu, da Sarkin Yakin Jama’a Alhaji…

Majalisar Masarautar Jama’a da ke Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna ta tube rawanin Sarkin Fadan Jama’a, Alhaji Abdullahi Zubairu, da Sarkin Yakin Jama’a Alhaji Bala Adamu da kuma Mainan Jama’a, Alhaji Adamu Muhammad bisa tuhumarsu da wasu laifuffuka  uku.

Sanarwar da babban hadimin ga Sarkin Jama’a, Alhaji Yakubu Isa (Dokajen Jama’a) ya sanya wa hannu ranar Alhamis ta ce ’yan majalisar karkashin jagorancin Sarkin Jama’a Alhaji Muhammadu Isa Muhammad II sun yanke shawarar daukar matakin tube musu rawunnan ne saboda laifukan da suka hada da rashin girmamawa da rashin ladabi ga sarkin da ’yan majalisarsa.

“An dauki wannan matakin a kansu ne saboda rashin ladabi da biyayya da rashin girmamawa ga Majalisar Masarautar Jama’a. Wannan ita ce matsayar da Majalisa ta dauka a kai,” in ji sanarwar.

Da yake yi wa Aminiya karin haske a kai, Dokajen Jama’a ya ce mutane biyun farkon an kwabe musu rawunna ne saboda su nadaddu ne.

Mutum na uku kuma an ba shi sarautar Maina ne amma ba a kai ga nada shi ba shi yasa aka ce an janye rawanin da aka ba shi.

Bisa ga binken Aminiya, wannan matakin shi ne irinsa na farko da Majalisar Masarautar Jama’a ta taba dauka kan wasu masu rawunna guda uku a lokaci daya.