Cibiyar samar da wutar lantarki ta Najeriya ta durkushe a karo na shida cikin watanni hudu a shekarar 2024.
Aminiya ta ruwaito cewa cibiyar samar da lantarkin ta durkushe ne da misalin karfe 2:42 na dare, kafin wayewar garin ranar Litinin.
Durkushewar ta sa karfin wutar lantarkin kasar ya ragu zuwa megawatt 64.70.
Hukumar kula samar wa lantarki ISO mai zaman kanta na nuni da cewa a halin yanzu tashar tana samar da wutar lantarki mai karfin 266.50mw daga tashoshin Okpai da Geregu da kuma Ibom.
- Ya Kashe ’Yan Mata 3 ’Yan Gida 1 A Yawon Sallah A Nasarawa
- An ceto sauran daliban Jami’ar Gusau da ’yan NYSC da ke hannun masu garkuwa
Wata sanarwa daga kamfanin rarraba wutar lantarki a Filato ta tabbatar da cewa “Katsewar da ake fuskanta a halin yanzu a Najeriya ta samo asali ne sakamakon raguwar karifn wutar lantarki daga cibiyar samarwa ta kasa da misalin karfe 02:42am na ranar Litinin 15 ga Afrilu, 2024”.
Sanarwar da shugaban sashen kula da harkokin kamfanoni, Dakta Friday Adakole Elijah, ya fitar, ta ce kamfani na sa ran a gyara matsotsar domin samar da wutar lantarki ga abokan hulda.