✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maryam Sanda ta daukaka kara bayan hukuncin kisa

Maryam Sanda, wacce babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yanke mata hukuncin kisa saboda  zargin laifn kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ta daukaka kara don…

Maryam Sanda, wacce babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yanke mata hukuncin kisa saboda  zargin laifn kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ta daukaka kara don neman kotun daukaka kara da ke Abuja ta janye hukuncin kisan da aka zartar mata a ranar 27 ga Janairun 2020.

Mai shari’a Yusuf Halilu ne ya yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar ratayewa.

A cikin takardar daukaka karar da ta gabatar wadda manyan lauyoyi ke jagoranta cikinsu akwai Rickey Tarfa, SAN.

A cikin takardar an bayyana cewa, hukuncin da aka yanke mata ya tauye mata ‘yanci, musamman yadda aka sauraron karar da abin da ya same ta sakamakon dogaro da hujjoji duk da irin shakkun da aka bayar ta hanyar shaidu, da kuma rashin bayanan sirri.