Nakasassu a Borno sun mayar da martani kan dokar hana barace-barace da gwamnatin jihar ta yi, ba tare da samar musu da mafita ba.
Gwamnatin jihar ta sanar da haramta barace-barace a kan tituna da zaman kashe wando a wasu wuraren, musamman a kananan hukumomin Maiduguri da Jere.
Farfesa Usman Tar, kwamishinan yada labarai na jihar, ya ce haramcin ya kuma shafi sauran kananan hukumomin jihar.
Shugaban kungiyar makafi a jihar, Muhammad Mustapha, ya ce, ya koka da cewa duk da dokar da ta tanadi a ware kashi 5 ga nakasassu wajen daukar ma’aikata, amma an yi watsi da su a kwanan nan da aka dauki malamai sama da 4,000 aiki a jihar.
Ya bayyana cewa a an yi watsi da su duk da cewa a cikinsu akwai nakasassu masu ilimi da za a iya daukarsu aikin koyarwa.
Mustapha ya kara da cewa, “idan ka ga nakasassu suna bara, dole ne ya sa suke hakan ba don son ran su ba.
Don haka yi kira ga gwamnati da ta samar da wasu hanyoyin rayuwa ga nakasassu kafin aiwatar da dokar hana barace-barace a kan tituna.
“Idan gwamnati ta dauki mataki irin wannan, muna sa ran cewa suna da wani shiri a gare mu,” in ji shi.
Ya kuma bayyana fatansu na ganin cewa gwamnati ta bullo da wani shiri na musamman a kansu bayan hana su bara.