✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe limami sun sace uwa da ’ya’yanta a Kaduna

’Yan bindiga sun kashe limami da mamu a cikin masallaci, suka yi awon gaba da matar aure da ’ya’yanta bayan sun kashe mijinta a garin…

’Yan bindiga sun kashe limani da wani mutum guda a cikin masallaci a yankin Ga Allah da ke gundumar Kakangi a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Sa’o’i kadan baya nan kuma ’yan bindiga suka kashe wani dan banga wa wani magidanci, suka yi awon gaba da matarsa da ’ya’yansa bayan sun jikkata wasu mutum uku a cikin garin Birnin Gwari.

Shugaban Kwamitin Cigaba da Samar da Tsaro a Birnin Gwari, Ibrahim Abubakar Nagwari, ya bayyana cewa ’yan bindigar sun sace mutane da dama a harin na biyu da suka kai da magariba a gidan mai a yankin Bagoma Dam da ke cikin garin.

“An kashe wani dan banga (Mu’awiyya) da wani dan gudun hijira daga kauyen Dagara, wasu mutum uku kuma sun samu rauni, amma suna samun sauki a Babban Asibitin Jibrin Maigwari da ke Birnin Gwari,” in ji shi.

Ya bayyana cewa ko kafin jami’an tsaro su zo su yi wa yankin kawanya, ’yan bindigar sun riga sun tsere.

Wani mazaunin yankin mai suna Muhammadu, ya shaida mana cewa da ’yan bindigar suka fice daga Bagoma sai suka far wa Anguwar Shakaru, inda suka kashe wani matsahi, suka yi awon gaba da matarsa da ’ya’yansa.

Shugaban Kungiyar Cigaba Masarautar Birnin Gwari (BEPU) Ishaq Kasai ya bayyana damuwa kan harin da aka kai gidan man na KBY.

An ruwaito wani basaraken yankin na Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Abdulrauf, yana rokon gwamnati ta karo tura jami’an tsaro a sassan karamar hukumar.

Ya kuma roke ta da ta ba wa jama’a izinin daukar bindiga don kare kansu, lura da yadda ’yan bindigar ke kara tsaurin ido suna shigowa har cikin gari su kawo hari.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga kakakikn ’yan sanda na Jihar Kaduna, Officer ASP Mansir Hassan amma hakarsa ba ta cim-ma ruwa ba.

Ya kira wayar jami’in, amma bai amsa kiran ba, haka ma rubutaccen sakon da aka tura masa babu amsa.