✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Martabar aikin jarida da kalubalen da ’yan jarida ke fuskanta

A shekara 10 da suka gabata, a duk kwana hudu ana kashe dan jarida.

Ba da jimawa ba ne aka gudanar da bukin ranar kare mutuncin ’yan jarida daga tsangwama da cin zarafi ta duniya, da nufin faɗakar da jama’a, musamman hukumomi da jami’an tsaro, muhimmancin tsare hakkokin dan jarida da masu neman labarai, da mutunta su.

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 2 ga watan Nuwamba na kowacce shekara ta zama ranar da za a rika haduwa ana tattauna muhimman batutuwan da suka shafi rayuwar manema labarai a fagen samar da bayanai.

Duk da irin rawar ganin da ’yan jarida ke takawa a fagen wayar da kan jama’a game da al’amuran da ke faruwa a kasashensu da sauran bangarorin duniya, har yanzu ana ci gaba da samun rahotannin kisa, dauri, ko cin zarafi da kuntata yanayin tsarin tafiyar da aiki, a sassa daban-daban na duniya.

Wata kungiya mai rajin kare hakkokin ’yan jarida ta Protect Journalists ita ma ta fitar da rahoton cewa, ’yan jarida da dama ne ke kulle a gidajen yari daban-daban na kasashen duniya.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya bayyana cewa, a duk bayan kwana hudu ana kashe dan jarida daya, a tsawon shekara goma da suka gabata, musamman a kasashen da ake fama da kalubalen tsaro da yake-yaƙe.

Rahotanni sun bayyana cewa a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2020 an kashe ’yan jarida kimanin dubu 12, a yayin da suke gudanar da aikinsu na neman rahotanni.

Gwagwarmayar da ’yan jarida ke sha wajen sadaukar da lokacinsu da rayuwarsu don ganin sun samar da muhimman bayanan da za su taimakawa al’umma, ta hanyar fadakar da su da wayar musu da kai game da yadda za su inganta rayuwarsu, ba karama ba ce.

Amma kuma abin takaicin shi ne kalilan ne daga cikin al’umma suke yaba wa da wannan kokarin nasu.

A wajen hukumomi kuwa ai ba su da wadanda suke kallo a matsayin rike-wuya ko barazana, kamar ’yan jarida.

Tun a shekarar 1972 da wata jaridar kasar Amurka ta Washington Post ta fara bankado abin fallasar nan na Watergate, wanda ya jawo murabus din Shugaba Richard Nixon, ’yan jarida suka zama abin tsoro a wajen ’yan siyasa da masu mulki.

’Yan jarida da dama a kasashen duniya daban-daban sun taimaka wajen kawo canje-canje masu ma’ana ta hanyar rubuce-rubuce ko shirye-shiryen da ake watsawa ta kafofin watsa labaransu, irin su matashin mai gabatar da shirin talabijin din nan na kasar Rasha, Edward Sagalaev, wanda a karshen shekarun 1980 ya kawo canji a siyasar kasar, wajen shirya muhawara da tattaunawa game da batutuwan da suka shafi makomar kasar, a karkashin shugabancin Gorbachev na wancan lokacin.

A nan Nijeriya ma rayuwar ’yan jarida da mutuncin aikinsu na ci gaba da fuskantar barazana iri-iri, daga wadanda ke kallon aikin nasu na yin karan-tsaye ga mulkinsu ko manufofin su na siyasa.

Kuma hakan ya jawo ’yan jarida da dama suka samu kansu a wani mawuyacin hali da ya hada har da kisa.

Na san ba za ku manta da batun zargin da aka yi wa tsohuwar gwamnatin mulkin soja ta Janar Ibrahim Babangida a shekarar 1986 ba, dangane da kisan gillar da aka yi wa tsohon editan mujallar Newswatch, Dele Giwa ta hanyar aika masa wasika mai ƙunshe da bom, kwana biyu bayan jami’an tsaron farin kaya na SSS sun yi masa wasu tambayoyi.

Ba a karƙashin gwamnatin mulkin soja ba, hatta a wannan mulkin na dimukuradiyyya ma ’yan jarida na ganin tasku iri-iri daga hannun jami’an tsaro da shugabanni da ke zargin su da hassala wutar rikice-rikicen kabilanci da siyasa wanda yanzu haka kasar nan ke fuskanta, ko kuma batun bata sunan gwamnati a idon talakawan kasa.

Ba za mu manta da wani abin takaici da ya faru ba na batun tsare wasu ’yan jarida hudu da ke aiki da Kamfanin  Jairdar Leadership, a lokacin mulki tsohuwar gwamnatin Shugaba Jonathan, don sun ki su bayyana hakikanin inda suka samo wani labari da jaridar ta buga da ke zargin tsohon shugaban da koƙarin ganin shirin da wasu jam’iyyun adawa ke yi na hadewa waje daya bai samu nasara ba.

Ban manta da abin da ya faru a shekarun baya ba, da editan jaridar Al-Mizan da wani wakilin jaridar game da wani rahoto da jaridar ta buga na cin zarafin jama’a da jami’an rundunar tsaron hadin gwiwa na JTF ke yi a garin Potiskum na Jihar Yobe ba, inda aka tsare su har fiye da mako guda, kuma aka muzguna wa iyalansu, duk da sunan yin bincike da tabbatar da tsaro.

Har kawo lokacin da nake wannan rubutu dan jarida Okechukwu Nnodim da ke aiki tare da jaridar PUNCH yana hannun masu garkuwa da mutane da ke neman kudin fansa har Naira Miliyan 10 kafin su sake shi. Bayan ya shafe tsawon watanni 8 a hannun ’yan ta’adda.

A Najeriya da wasu kasashen da ke cikin fitinar ta’addanci irin wannan rayuwa ce ’yan jarida ke fuskanta, bayan kunci da tsananin da suke rayuwa a ciki na rashin kyan albashi da rashin muhallin da ya dace na gudanar da aiki.

Wannan hali da ’yan jaridar Najeriya da wasu kasashe masu tasowa ke fuskanta ya sa Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin kasar Amurka ke tsawatar wa gwamnatoci da kwamandojin yaki a fagagen fama daban-daban, game da bukatar sakar wa ’yan jarida mara su gudanar da aikin su cikin ’yanci da aminci!

Yayin da muke kara jinjina da yabawa ga irin rawar ganin da ’yan jarida ke takawa, muna kuma fatan ganin canje-canje na cigaban aikin jarida, da ya hada da inganta muhallin aiki, da kyautata albashi da sauransu.