Dalibar nan da ’yan bindiga suka kashe bayan sun yi garkuwa da ita da ’yan uwanta, NabeehaAl-Kadriyah, ta kammala karatun digirinta a matakin farko (First Class) a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya.
Kawun Marigayiya Nabeeha mai suna Sherifdeen ya ce bayanan da suka samu gabanin bikin yaye daliban jami’ar suna cewa marigayiyar ta samu ‘First Class’.
A cewarsa, da ba a kashe ta ba, da ta sami lambar yabo a taron yaye dalibai na jami’ar da za a gudanar ranar Asabar din nan, 27 ga wannan Janairu, 2024.
“Da a ce tana raye da ta shaida wannan taron. Sai dai lamarin ya kara karfafa imaninmu ga Allah Madaukakin Sarki.
- Filato: An sa dokar hana fita na sa’a 24 a Mangu
- Mutane 25,490 Isra’ila ta kashe a Gaza —Ma’aikatar Lafiya
“Muna godiya ga duk wadanda suka tsaya mana a wannan jarabawa.”
Malam Sherifdeen wanda shi ne ya je dauko gawar bayan an yi wa dalibar kisan gilla ya ce, “An yi mata kisan gilla ne, aka tilasta wa kanwarta, Najeeba ganin gawarta cikin yanayi mai tsanani domin kawai mu gaggauta biyan kuɗin fansa.”
A cewarsa, sakin sauran kannen Nabeeha da aka yi a yammacin ranar Asabar ya jefa danginta cikin zullumi.
Wakilinmu ya ziyarci iyalan a gidansu da ke garin Ilori a Jihar Kwara, inda har yanzu ake zuwa musu jaje.