✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maria Sharapoba ta yi wa kanta tonon silili

Shahararriyar ’yar kwallon Tenis da ke Rasha Maria Sharapoba ta yi wa kanta tonon silili bayan ta amince da yin amfani da kwayoyi masu kara…

Shahararriyar ’yar kwallon Tenis da ke Rasha Maria Sharapoba ta yi wa kanta tonon silili bayan ta amince da yin amfani da kwayoyi masu kara kuzari a lokacin wasa.  Ta yi wannan furuci ne jim kadan bayan Hukumar yi wa ’yan kwallon Tenis gwaji ta same ta da laifin yin amfani da kwaya mai sanya kuzari a wani bincike da ta yi mata a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da ake gasar tenis ta Austireliya da ake wa lakabi da Austrelian Open.
Sharapoba ’yar asalin Rasha  ta ce ba wannan ne karon farko da ta taba yin amfani da kwaya mai sanya kuzari a wasan  kwallon tenis ba, sai dai a wannan karo ne dubunta ta cika.
Wannan furuci da ta yi ya ba jama’a da dama mamaki, inda wasu suka rika mamakin yadda ta fallasa kanta da kanta yayin da wasu kuma ciki har da shahararriyar ’yar kwallon Tenis da ke Amurka Serena Williams suka yaba mata a kan wannan namijin kokarin da ta yi na fallasa kanta.
Sai dai rahotannin da ke fitowa sun nuna tuni wasu daga cikin kamfanonin da ke huldar arziki da ita suka fara soke kwangilar yin tallar da suka ba ta na miliyoyin daloli.  Ya zuwa ranar Talatar da ta wuce kamfanin Nike da na kera motoci mai suna Porsche sun soke kwangilar da suka ba ’yar kwallon tenis din saboda wannan abin kunya.  Sannan ana sa ran nan gaba kadan su ma wadansu kamfanonin da suke daukar nauyinta za su sanar da daina yin hulda da ita.
Kamfanonin sun nuna babu yadda za a yi su cigaba da hulda da ita ganin cewa ta nuna ba ta da gaskiya kuma cigaba da hulda da ita zai iya janyo musu asara.
Rahoton ya nuna Maria Sharapoba tana samun kudin shigar da suka kai Dala miliyan 29.7 kwatankwacin Naira biliyan 9 da miliyan 400 a shekara, kuma fiye da rabin kudin tana samunsu ne ta bangaren yi wa kamfanoni tallace-tallace.
Wannan ta sa masana harkar tattalin arziki suka fara hasashen cewa ’yar kwallon za ta shiga halin tasku ganin yadda kamfanoni da dama suka rika rububin rabuwa da ita tun bayan da ta yi wannan tonon silili.
Idan hukumar kula da tenis ta samu ’yar kwallo da laifi akwai yiwuwar a dage ta daga shiga harkokin wasanni har na tsawon shekara 4.
Maria Sharapoba tana daya daga cikin matan da suka yi fice a bangaren kwallon Tenis a duniya.  Hasalima tana daga cikin sahun matan da suka fi samun kudin shiga a duk shekara.