✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maradona ya nemi ’yan sanda su kama iyalinsa

Shahrarren dan kwallon Ajantina Diego Maradona ya zargi matarsa da ’ya’yansa a kan suna da hannu wajen sace masa kudin da suka kai Fam Miliyan…

Shahrarren dan kwallon Ajantina Diego Maradona ya zargi matarsa da ’ya’yansa a kan suna da hannu wajen sace masa kudin da suka kai Fam Miliyan 3 da dubu 400 kwatankwacin Naira Biliyan 1 da miliyan 625 da dubu 200.

Tsohon dan kwallon yana da yakinin bayan sun yi masa satar sun kai ajiyar kudin a wani banki ne da ke Uruguay inda daga baya suka yi amfani da kudin wajen sayen gidaje da kadarori a Amurka.

A kan haka ne Maradona ya nemi ’yan sanda su kama ’yarsa Gianina da yake zargin ita ce kanwa uwar gami don su gudanar da kwakkwaran bincike a kanta don a dawo masa da kudinsa.  Haka kuma dan kwallon ya zargi matarsa da laifin hada baki da ’ya’yansa mata biyu wajen yi masa satar.

Maradona, mai shekara 57 an nuna tuni ya shigar da kara a gaban wata kotu don a tuhimi tsohuwar matarsa Claudia bilafane da ’ya’yansa mata biyu Dalma da Gianina game da yadda suka hada baki wajen sace masa wadannan kudade a lokacin da yake tare da uwarsu.

Ya ce yana da tabbacin bayan sun sace masa kudin kuma sun ajiye su a wani Banki da ke Uruguay, daga baya sun yi amfani da kudin wajen sayen gidaje da kuma kadarori a kasar Amurka.

Wata jarida da ke watsa labaran wasanni a kasar Sifen mai suna Marca ta kalato yadda ’yar Maradona Gianina ta kai ziyara Uruguay a watan Agustan bana da hakan ya nuna akwai rina a kaba.

A tattaunawar da aka yi da ’yarsa Gianina a game da zargin da mahaifinsu Maradona yake yi musu na sace masa makudan kudi ta ce “ai jami’an tsaron sun san inda nake don haka ina jira su zo su kama ni in da gaske mahaifina yake yi game da wannan zargi”.

Yanzu haka Diego Maradona yana horarwa ne a wani kulob da ke Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) mai suna Al-Ain.