A ranar Laraba 20 ga watan nan da muke ciki ne Babbar Kotu da ke Abuja ta yanke hukuncin soke kungiyar fafutukar kafa yankin Biyafara (IPOB) a duk fadin kasar nan. Kotun ta yi haka ne bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar mata da bukatar hakan.
Mukaddashin Alkalin Babbar Kotun ta kasa Mai Shari’a Abdu Kafarati ne ya yanke wannan hukunci. Ya ce ayyukan da kungiyar IPOB take yi a kasar nan sun saba wa dokar kasa, hasalima suna neman tayar da husuma ne da kuma kokarin wargaza hadin kan kasar nan.
Lauyoyin da suka tsayawa gwamnatin tarayya a kotun sun hada da Babban Mai Shari’a na kasa Abubakar Malami(SAN) da Babban Sakatare a Ma’aikatar Shari’a ta kasa Mista Dayo Apata da kuma wasu gungun lauyoyi.
Lauyoyin sun nuna wa kotun kungiyar IPOB ta zama kungiyar ’yan ta’adda da hakan ya saba wa dokar kasa ta 2013 kuma ya dace a saurari wannan shari’ar ce a asirce ba a bainar jama’a ba.
A yayin yanke hukunci, alkalin babbar kotun ya ce “kotun ta soke kungiyar IPOB wajen gudanar da ayyukanta a kowane bangare na kasar nan musamman a yankin Kudu maso Gabas da kuma Kudu maso Kudu. Sannan kotun ta ce haramun ne wani ko wata kungiya ta rika yin hulda da kungiyar IPOB.
Jim kadan bayan an zartar da wannan hukunci ne sai Ministan Shari’a na kasa Abubakar Malami ya fito karara ya bayyana cewa an soke kungiyar IPOB. Ya ce kotu ta yi haka ne bayan ta samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ya ce wannan hukunci shi ne na karshe don babu wani hurumi na daukaka kara, don al’amari ne da ya shafi yunkurin wargaza kasa da kuma ta’addanci.
Kafin nan, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a soke kungiyar IPOB kamar yadda Gwamnonin da ke yankin Kudu maso Gabas da na Kudu maso Kudu suka bayar da umarnin soke harkokin kungiyar jim kadan bayan sojoji sun bayyana kungiyar a matsayin haramtacciya.
Sai dai kalaman da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki ya yi na cewa sojoji ba su bi ka’ida wajen soke al’amarun kungiyar IPOB ba, ya janyo ce-ce-ku-ce. Saraki ya ce “na tabbata ba a bi ka’ida wajen soke kungiyar IPOB ba kuma ina fata shugaban kasa zai bi dokar kasa wajen bin ka’ida kafin ya soke kungiyar”.
Sai dai kalaman da Saraki ya yi sun taimakawa gwamnati wajen bin ka’ida kafin a soke kungiyar, ba kamar yadda wadansu suka zata tun da farko cewa Sarakin yana goyon bayan kungiyar ne.
Mun yaba da matakin da aka dauka na soke wannan kungiya ganin yadda harkokinta suke neman wargaza kan kasar nan da kuma yunkurin janyo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma. Bai kamata gwamnati ta rika kyale irin wannan kungiya mai neman tayar da hankali a kasa ba tare da tana taka mata birki ba.
Ministan Yada Labarai Alhaji Lai Mohammed ya ce rahotanni sun nuna kungiyar tana samun tallafi ne daga barayin gwamnati da kuma wadansu kasashen waje irin su Faransa. “kungiyar IPOB tana samun kudin gudanar da ayyukanta ne daga hedkwatarta da ke Faransa… ina kyautata zaton ’yan Najeriya mazauna can ne suka yin karo-karo wajen tafiyar da al’amurran wannan kungiya. In ba haka ba a ina shugabansu Nnamdi Kanu yake samun kudin gudanar da wannan kungiya? Wannan shi ne gaskiyar magana”.
Minista Lai Mohammed ya kara da cewa, a baya gwamnatin tarayya ta nemi Ingila ta rufe Gidan Rediyon Biyafara da ke Landan, kafar watsa labaran da Nnamdi Kanu yake amfani da ita wajen harzuka magoya bayansa amma abin mamaki sai kasar ta yi biris da wannan bukata. Ingila ta nuna ta yi haka ne don a ba kowane dan Adam ’yancin fadin albarkacin bakinsa.
Amma daga rahotannin da ke fitowa Ingila ta ce gwamnatin tarayya ba ta aika mata wannan bukata ba. Ko ma dai mene ne muna kira ga gwamnatin tarayya da ta gabatar da wannan bukata a wannan lokaci. Mun tabbata Ingila ba za ta so ganin Najeriya ta shiga halin rudani saboda son ran wani ko wasu tsiraru ba.
Kawo yanzu Lauyan IPOB Ifeanyi Ejiofor yana kokarin daukaka karar soke kungiyar da kotu ta yi ne, don haka muna kira ga gwamnatin tarayya da lallai ta jajirce wajen ganin hakan ba ta yiwu ba.
Ba za mu amince da fakewa da wasu ke yi da dokar bai wa ’yan kasa ’yanci wajen kawo rudani da tashn hankali ga ’yan Najeriya da aka kiyasta yawansu ya kai kimanin miliyan 180 ba.