✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maraba da dawowar Kamfanin Tumatir na Dangote

A makon jiya wani labari mai dadi ya bazu a kasar nan bayan rukunin Kamfanin Dangote ya sake bude Kamfanin Tumatirinsa da ke Kadawa a…

A makon jiya wani labari mai dadi ya bazu a kasar nan bayan rukunin Kamfanin Dangote ya sake bude Kamfanin Tumatirinsa da ke Kadawa a Jihar Kano wanda aka rufe shi kimanin shekara biyu da suka wuce.

Kimanin shekara biyu ke nan da kamfanin ya dakatar da aiki jim kadan bayan an kaddamar da shi. Hakan ya faru ne saboda rashin isasshen tumatir da kamfanin ke samu daga manoma da yadda kamfanin ya samu rashin jituwa kan yadda yake sayen tumaturi daga wajen manoma.

Kamfanin Tumatir na Dangote an ce shi ne mafi girma a Nahiyar Afirka. Ya samu tsaiko ne jim kadan bayan ya fara aiki a tsakanin shekara daya da wata biyar saboda matsalolin da aka zayyano a sama.  Rahotanni sun nuna kamfanin yana da karfin samar da tumaturin gwangwani akalla tan1,200 a kowace rana.

Manajan Daraktan Kamfanin Abdulkarim Kaita a wata sanarwa da ya fitar ya ce “Babban kalubalen da kamfanin ke fuskanta shi ne na rashin samun isasshen tumaturi daga wajen manoma da zai ba da damar a rika sarrafawa a kullum.  A wancan lokaci da muka fara aiki, mun lura manoman yankin ba za su iya samar mana da isasshen tumaturin da za mu rika sarrafawa a kullum ba.  Haka mun samu matsalar daidaito a kan farashin da ya dace mu rika sayen kowane kwandon tumatir daga wajen manoman.  Wadannan da wasu dalilai na daga cikin abin da ya sa kamfanin ya dakatar da aiki jim kadan bayan an kaddamar da shi.”

Ya kara da cewa a yanzu kamfanin ya dauki matakin ware wata katafariyar gona don shuka tumatir don ganin ba a sake samun irin waccan matsala a nan gaba ba. Ya ce kamfanin zai rika noma tan 60 a kowace hekta yayin da ake sa ran manoman yankin kuma za su rika noma tan 10 a kowace hekta don ganin ba a sake samun wani tsaiko ba.

Aminiya ta jinjina wa Rukunin Kamfanonin Dangote na sake farfado da kamfanin tumatir din da ke Jihar Kano saboda muhimmancin da yake da shi wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan. Ya dace a yi duk mai yiwuwa don ganin kamfanin bai durkushe ba. Kamfani ne da zai samar da ayyukan yi musamman ga manoma da kuma kudin shiga ga kasar nan.

Yunkurin da Gwamnatin Tarayya ke yi na hana shigo da tumaturin gwangwani daga ketare ba zai yiwu ba, har sai an karfafa wa kamfanin sarrafa tumatir na Dangote gwiwa ta hanyar ba shi cikakken tallafi da kuma goyon baya.

Idan kamfanin zai rika samar da isasshen tumaturin gwangwani a kowace rana don amfanin al’ummar kasar nan ko shakka babu Gwamnatin Tarayya za ta iya cimma burinta na hana shigo da tumaturin gwangwani daga ketare. Sai dai yadda Gwamnatin Tarayya ke babatu wajen hana shigo da tumaturin gwangwani daga waje da yadda ta yi biris wajen karfafa wa kamfanonin cikin gida wajen samar da tumaturin ya zama tamkar tana yin fargar jaji ne.  Ta yaya za a hana shigo da tumatir daga waje amma a bangare daya ta  ki daukar matakin wadata kasar nan da shi a cikin gida?

Matsalar da manoman tumatir suke fuskanta ta lalacewarsa a lokacin kaka za ta kau idan Kamfanin Tumatir na Dangote ya dore.  Don haka a tsakanin manoman da kuma Kamfanin Dangoten za a ci riba biyu ta kowace fuska.  Yayin da kamfanin zai samu isasshen tumaturin da zai rika sarrafawa su kuwa manoman za su rika samun damar sayar da tumaturinsu a kan farashin da ya dace ba tare da sun samu faduwa ko lalacewa ba, haka kuma kasar nan za ta rika samun kudin shiga mai yawa daga waje.

Sannan wata ribar ita ce yadda za a rage dimbin matsalolin samun ayyukan yi a kasar nan.  Hakan zai ba matasa damar rungumar harkar noman tumatir maimakon zaman kashe wando.

Bincike ya nuna Najeriya tana da kasar yin kowane irin noma baya ga kyakkyawan yanayi don haka babu dalilin da zai sa a rika samun karancin manoman tumatir a kasar nan.

Don haka muna kira ga Gwamnatin Tarayya ta bullo da hanyoyin tallafa wa kamfanoni irin na Dangote da kuma manoma don ganin an cimma burin samar da isasshen tumatir a kasar nan.  Ya dace gwamnati ta yi amfani da Bankin Masana’antu (Bank of Industries) ko Bankin Manoma (Bank of Agriculture) don samar da rance don ganin noman tumatir ya bunkasa a kasar nan, hakan zai ba Kamfanin Tumatir na Dangote ci gaba da dorewa har na tsawon lokaci ba tare da an samu wani tsaiko ba.

Muna fata Kamfanin Dangote zai dore ba tare da ya sake fuskantar wata matsala da za ta sa ya dakatar da aiki nan gaba ba.