✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mara lafiya ya sace motar daukar gawa a Kano

’Yan sanda sun kama barawon motar ne a kauyen Takwasa a Jihar Jigawa

Wani mara lafiya mai karaya a kafarsa ya sace motar daukar marasa lafiya da magungunan da ke cinta a Jihar Kano.

’Yan sanda sun kama barawon motar daukar marasa lafiyan ne a kauyen Takwasa na Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa a yayin da yake kokarin tserewa da ita.

Kakakin ’yan sandan jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu, ya ce “’Yan sanda sun gano motar ce a kauyen Takwasa ta Karamar Hukumar Babura a Jihar Jigawa, a hannun wani mutum dan asalin Karamar Hukumar Daura ta Jihar Katsina, mai muguwar karaya a kafarsa.”

Ya ce an yi sanar gano motar ce bayan samun rahoton, “sace wata motar daukar marasa lafiya — kirar ‘Hummer Bus’ mara lamba a jikinta— da magungunan da ke cikinta, mallakin Karamar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano, a kauyen Kanya Hore da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa ta Jihar Kano.

Daga nan ne ’yan sanda daga Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa suka dukufa aiki, inda washegari suka gano ta da misalin karfe 8 na safiyar ranar Litinin 11 ga watan Disamban da muke ciki.

Ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kafin fa gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.