✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mara kafafu ta zama zakara a gasar motsa jiki a Amurka

Wata yarinya ’yar kimanin shekara 27 mai suna Jen Bricker wacce ba ta da kafafu ta zama zakara a gasar motsa jiki watau (gymnastics) a…

Wata yarinya ’yar kimanin shekara 27 mai suna Jen Bricker wacce ba ta da kafafu ta zama zakara a gasar motsa jiki watau (gymnastics) a Amurka.
Ita dai wannan yarinyar an haifeta ne ba tare da kafafu ba, ta taso a garin Illinois da ke yankin Oblong na Amurka kuma ba ta yarda nakasar da ta same ta ta hana ta shiga harkokin wasanni don a dama da ita ba.
Tun tana karama ta yi fice a wasan kwallon hannu na bolleyball da na kwallon kwando Basketball da na motsa jiki gymnastic duk da rashin kaf afunta.
Ta fara yin atisaye ne a shimfidar tampolin a lokacin da take karama kafin ta kwarr ta fara shiga ana damawa da ita a wasanni motsa jiki daban-daban.
kwazon da take nunawa a harkar motsa jiki na gymnastic ne ya ja hankalin kwararren dan Amurka a mai wasan motsa jiki wanda ya lashe wa kasar lambar zinare a gasar  Olamfik a shekarar 1996 Dominikue Mocceamu ya zama kocinta.
A karshen makon jiya ne Misis Jen Bricker ta zama zakara a gasar jimnastik a Amurka bayan ta doke abokan hamayyarta masu kakafu  inda ta samu yabo lambar yabo. Hakan ta sa samun yabo daga sassan duniya musamman ganin yadda a matsayin wacce ba ta da kafafu ta yi wa sauran zarra.
Ta yi murnar samun wannan nasara kuma ta sha alwashin wakiltar Amurka a wasan motsa jiki na jimnastik a gasar Olamfik mai zuwa.