✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (17)

Darasi na Ashirin da Biyu Ci gaba da tuntubar kabilun da ke wajen Makka Kariyar da Annabi (SAW) ya samu daga Mut’im Ibn Adiyyu a…

Darasi na Ashirin da Biyu

Ci gaba da tuntubar kabilun da ke wajen Makka Kariyar da Annabi (SAW) ya samu daga Mut’im Ibn Adiyyu a dawowarsa daga Da’ifa ta samar masa ’yar sararawa daga tsangwamar mutanen Makka, sannan ta ba shi damar mai da hankali wajen neman hanyoyin fitar da sakonsa waje tare da neman masu taimaka masa. A wannan lokaci Annabi (SAW) ya ba da karfinsa wajen neman hanyoyin kulla alaka da mutanen da ke wajen Makka, wanda kuma wannan na daga cikin dalilin da suka sa ya fita zuwa garin Da’ifa. Alal hakika, malaman tarihi sun ce Manzon Allah (SAW) ya fara fuskantar da tuntubarsa zuwa waje da Makka ne tun lokacin da mutanen Makka suka sanya wa Banu Hashim takunkumin kaurace wa al’amuransu.

Saboda haka Annabi (SAW) ya mai da hankali wajen ganawa da masu zuwa Aikin Hajji garin Makka daga sauran nahiyoyin kashashen Larabawa. A irin wannan yunkuri ne aka samu mutane shida daga garin Madina (Yasrib) suka musulunta a shekara ta goma sha daya da aiko Annabi (SAW). Wannan ya samu ne sakamakon tuntubar kabilun Larabawa da Annabi (SAW) yake yi shekara-shekara a lokutansu na Aikin Hajji.

Annabi (SAW) ya shiga bin mahajjata har zuwa hemominsu a filin Mina don ganawa da jagororin kabilun Larabawa, musamman saboda ya kira su zuwa ga addinin Musulunci kuma ya nemi kariya daga gare su tare da mika kansa don bukatar mafaka inda zai samu sararin ci gaba da isar da sakon Musulunci. Amma a duk inda Annabi (SAW) ya sa kafarsa, bayan ya gama ganawa da jama’a ya fito sai Abu Lahab ya shiga ya warware abin da Annabi (SAW) ya kulla ta hanyar karyata shi da yi masa sharri.

Haka Annabi (SAW) ya ci gaba da aikinsa na yada addinin Musulunci; a wani wurin in ya je a yi watsi da abin da ya je da shi kuma a karyata shi nan take, a wani wurin kuma sukan jinjina maganar Annabi (SAW) a tsanake ko su nemi sanya masa wasu sharudda da za su amfanar da kabilarsu. Akwai misali kabilar Banu Hanifah da suka kori Annabi (SAW) da ya je ganawa da su a hemarsu a Mina tare da tsanantawa a kansa. Wannan kuwa ita ce kabilar da Musailamah Al-Kazzab ya fito wanda shi ne ya bijire wa Sayyidina Abubakar (RA), bayan rasuwar Annabi (SAW) ya yi kuma da’awar annabta. Su kuma kabilar Banu Amir Ibn Sa’asa’ah sun nemi ne su san irin moriyar da za su samu idan sun bai wa Annabi (SAW) kariya da goyon baya. Suna so su san cewa shin zai taimaka musu, kasar Larabawa baki daya ta koma karkashinsu ko kuma ya amince musu da cewa su ne za su gaje shi a annabci bayan ya bari. Amma sai Annabi (SAW) ya ce musu karfin ikon mallaka musu kasar Larabawa ba a hannunsa yake ba, a Hannun Allah yake. Haka su ma mutanen Banu Kindah suka nemi bukatar gadon gurbin Annabi (SAW) bayansa idan har suka karbe shi tare da ba shi kariya da mafaka. A wasu lokuta ma Annabi (SAW) ya bi kwararo-kwararon hemomin kabilun Larabawa yana shela cewa “Shin akwai wadanda za su dauke ni (in bi su) zuwa kasashensu?” Haka su ma sahabban Manzon Allah (SAW) irin su Abubakar as-Siddik da Zaid Ibn Haris sun taimaka masa ta hanyar tunkarar wasu kabilu don mika bukatar Annabi (SAW) da da’awar Musulunci gare su.

Daga cikin kabilun da Annabi (SAW) ya tuntuba har da kabilun Awsu da Khazraj da ke garin Madina (wacce a lokacin ake kiranta da sunan Yasrib). Malaman tarihi sun ce fara ganawar Annabi (SAW) da mutanen Madina ta auku ne tun kimanin shekara hudu ko biyar Kafin Hijira, wato tun lokacin da kabilar Banu Hashim suke karkashin takunkumi da kauracewa daga mutanen Makka. Bangarori da dama daga mutanen Madina sun zo sun saurari Annabi (SAW) a lokuta daban-daban, amma wadanda suka fara karbar addinin Musulunci bisa daya daga cikin ruwayoyi, su ne As’ad Ibn Zurarah da Zakwan Ibn Asd Kays. Wadannan bayin Allah sun kasance tun gabanin haduwa da Manzon Allah (SAW) suna sha’awar addinin kadaita Allah wajen bauta, sabanin abin da mutanensu suke kai na bautar gumaka. Irin wadannan nasarori da Manzon Allah (SAW) ya fara samu, su ne suka bade kofar shiga Madina ga Manzon Allah (SAW).

Darasi na Ashirin da Uku

Kewayawar Annabi ga kabilun Larabawa don neman taimako da mafaka Ya kasance tunda Allah (SWT) Ya umarci Manzon Allah (SAW) da bayyana da’awarsa yana fita lokacin kwanukan kasuwannin Larabawa kafin aikin Hajji, yakan je masaukansu yana kiransu kabila-kabila zuwa ga Musulunci, wadannan kasuwanni mafiya shahararsu uku ne su ne:

Kasuwar Ukaza;

Kasuwar Mujanna;

kasuwar Zul-Majaz.

Ukaza: Wata alkarya ce da ke tsakanin Nihlah da Da’ifa ana cin wannan kasuwa daga ranar 1 zuwa 20 ga watan Zul- Kidan kowace shekara.

Mujanna: Kuma daga 20 zuwa karshen watan.

Zul-Majaz: Kuma daga 1 zuwa 8 ga Zul-Hajji, sannan a shiga ayyukan Hajji irin nasu na wancan lokaci.

A wannan lokacin Annabi (SAW) yana kiransu kuma ya bijiro musu da kansa a kan su jibance shi su taimaka masa, sai dai babu wanda ya amsa masa, wadansu su yi magana mai dadi, wadansu su yi masa mummunar magana wani ma ya shardanta masa shugabanci ya dawo kansa a bayansa, in dai ya yarda to sai a taimaka masa. Wani ma ya ce masa me ya sa danginka suka ki bin ka? Cikin wadanda suka fi munana masa magana su ne mutanen Musailamatul Kazzab.

Ana cikin wannan lokaci na kunci da mawuyacin hali da kiran Annabi (SAW) yake fuskanta domin duk kabilun Makka sun juya masa baya, sai Allah Ya kaddara wadansu kuma su gane gaskiya, daga cikinsu wani mawaki, kuma mai daraja a cikin mutanensa mutumin Yasriba ( Madina) ya zo Makka sunansa Suwaid dan Samut ya karbi Musulunci. Da zai zo sai ya bijiro wa Annabi (SAW) irin hikimar Lukman, shi ma ya bijirar masa da Kur’ani, da ya ji sai ya musulunta, sai dai wannan mutum an kashe shi a yakin da kabilar Aws da Khazraj suka yi. Haka akwai Iyas dan Mu’az shi ma daga Madina yake, matashi ne ya zo Makka a farko-farkon shekara ta 11 da aiko Annabi (SAW), da ya ji kiran Annabi (SAW) ya ce wallahi wannan ya fi alheri a kan abin da muka zo yi. Sai wani babba ya kwabe bakinsa, shi ma ya rasu bayan dawowarsu, sai dai lokacin da mutuwarsa ya yi an ji yana ta yin hailala da kabbara da tasbihi wanda mutanensa ba su yi tantama ba ya yi imani kuma ya mutu Musulmi.

Abu-Zar mutumin Gifari: Shi ma a dalilin musuluntar wadannan ta sa ya aiko dan uwansa ya je Makka ya ji gaskiyar wannan addini, da ya dawo ba wani gamsasshen bayani sai ya tafi da kansa. Ya zo Makka sai dai shi bai nemi kowa ya kai shi wurin Annabi (SAW) ba, ya dai zauna a harami ne na tsawon wata daya ruwan Zam-Zam kawai yake sha, shi ne abincinsa har a hankali wata rana ya bi Aliyu (RA) a baya ya kai shi inda Manzon Allah (SAW) yake. Ya je ya nemi ya bijiro masa da ainihin Musulunci ya bayyana masa sai ya musulunta, yana fitowa ya je bainar jama’a a Masallacin Harami ya furta kalmar shahada a fili take Kuraishawa suka hau dukansa da kyar Abbas (RA) ya kwace shi. Washegari bai fasa ba, bai ji tsoro ba, ya sake fadar wannan kalma wadda take tayar da hankalin mushirikai nan ma suka sake yi masa duka. Abbas ya sake ceto shi kamar dai jiya, sannan ya koma garinsu, yana jin Annabi (SAW) ya yi hijira zuwa Madina shi ma ya yi hijira Madina.

Za iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141, email:[email protected]