✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan ’Yan Siyasa 10 Da Aka Daina Jin Duriyarsu

Duk da shuhura da karfin fada a ji da suka samu a baya, yanzu an daina jin duriyarsu

A shekaru 25 na dawowar mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya, an yi waɗansu fitattun ’yan siyasa masu karfi daga sassan, da yawa sun ci gaba da kasancewa masu rinjaye yayin da wasun su kuma zamani ya ajiye su, haskensu ya dusashe a siyasa.

Waɗannan ’yan siyasa sun taɓa riƙe manyan madafun iko a jamhuriya ta huɗu, amma yanzu kusan an manta da su, sai a babin tarihi.

Wasu daga cikinsu siyasar ta yi musu ritayar dole, wasu kuma shekarunsu sun ja da yawa, don haka girma ya cin musu, sun koma gefe sun zama ’yan kallo.

Salihu Mahmud Dantata wani masani kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, ya bayyana dalilai uku a da suka sa ’yan siyasar da a da suke faɗa aji suka kuma ’yan kallo.

Ya ce akwai,  “Cin hanci ga kuma son rai da duk wanda ya yi nasara to burinsa ya kawar da tarihin kowa, sai kuma lalacewar tarbiyya da ta samu gindin zama a fagen siyasa.”

Dantata ya ce, duk da cewa ana buƙatar sabbin jini a fagen siyasa da mulki, dole ne in ana son cigaba a riƙa surkawa da gogaggu wadanda suka ga jiya suka ga yau.

Wannan rahoto ya rairayo wasu manyan ’yan siyasa 10 da a wani lokaci kadan da ya shude ludayensu ke kan dawo, amma a yanzu sai dai kallo, duk kuwa da cewa suna raye.

1. Salisu Buhari

Ba domin wata karya da Ibrahim Salisu Buhari ya sharara ba, da ya zama shugaban majalisar wakilai mafi karancin shekaru a Najeriya.

Sai dai kash! Ya taka doka idan ya yi karyar cewa shekarunsa 36 maimakon 29 a farkon jamhuriya ta hudu.

Salisu Buhari ya zama shugaban majalisar wakilai, amma bayan makonni shida kacal, dambarwa ta kunno kai kan asalin shekarunsa na gaskiya da kuma abin da ya bayyana.

Yana da shekara 29 a duniya, amma ya ce shekarunsa 36, sannan ya ce ya samu shaidar difloma a fannin Akanta a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, a shekarar 1988, ya yi digirin digirgir a fannin kasuwanci da gudanarwa daga Jami’ar Toronto, Kanada, a 1990, sai bautar Kasa a Kano a 1991.

Bayan gudanar da bincike, an gano akwai shifcin gizo a cikin bayanan na Salisu Buhari, inda kafofin yada labarai suka saka shi gaba, dole ya hakura da kujerarsa ta wakilcin mazabar Nasarawa a zauren majalisar.

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya yafe masa, amma har zuwa yanzu, babu wata kujera da Salisu ya sake samu da za a ce ya dawo an dama da shi.

2. Bamanga tukur

Akwai da dama dake ganin irin Bamanga Tukur ba su da yawa a cikin ma’aikatan gwamnatin tarayya, domin kuwa ya jima ludayensa na bisa dawo.

Dan kasuwa ne, mai fadi a ji, kuma ɗan siyasa.

Shi ne tsohon gwamnan tsohuwar jihar Gongola ne, tsohon ministan masana’antu, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, tsohon shugaban kungiyar New Partnership for African Development (NEPAD), kuma tsohon shugaban zartaswan kasuwanci na Afrika.

Bamanga ya ga tasku a lokacin shugabancinsa a PDP tsakanin 2012 zuwa 2014, inda aka yi fama rigingimun cikin gida a jam’iyyar, har ya kai ga sauya shekar  gwamnonin PDP biyar zuwa jam’iyyar  adawa ta APC.

Yau Bamanga Tukur yana da shekaru 88 a duniya, ana kyautata zaton ya yi ritaya daga harkokin siyasa da ma na jama’a, ya bar wa masu tasowa, a ciki har da dansa, wanda yanzu shi ne sakataren gwamnatin jihar Adamawa.

Sai dai duk da wadannan nasarori na Bamanga, yanzu ana neman mantawa da shi, duk da cewa yana raye.

3. Oladimeji Bankole

Dimeji Bankole, ya shugabanci majalisar wakilai kuma babban dan siyasa ne  amatakin kasa.

Bankole ya zama dan kasar mai muƙami na  hudu bayan murabus din, Patricia Etteh.

Ya wakilci mazabar tarayya ta Abeokuta ta Kudu tsakanin 2002 zuwa 2007 a karkashin jam’iyyar PDP.

Natsuwarsa da salon jagorancinsa ya sa ana girmama shi.

Amma kamar yadda wasu masu fada a ji a siyasar Najeriya, wa’adinsa ya kare da zarge-zarge 16 daga hukumar EFCC, kan badakalar aringizon kwangiloli da almundahanar kudaden gwamnati da suka kai Naira biliyan tara.

Tuni dai kotu ta wanke shi.

A 2019 ya tsaya takarar gwamnan jihar Ogun a karkashin jam’iyyar ADP, amma ya sha kaye.

Ya yi yunkurin komawa APC a 2022 kuma ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar, amma daga baya ya hakura ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yakin neman zabe.

4. Adamu Mu’azu

Adamu Muazu ya kasance daya daga cikin gwamnonin da suka fi taka rawar gani a Najeriya tsakanin 1999 zuwa 2007.

Ana kuma yi masa kallon daya daga cikin masu biyayya ga Shugaba Olusegun Obasanjo, wanda da dama ke tunanin zai gaje shi.

A lokacin da Obasanjo ya zabi Marigayi Shugaba Umaru YarAduwa a matsayin wanda zai gaje shi, nan take masu ra’ayin tsayawa takara  suka janye aniyarsu, sai dai an ce Adamu Mu’azu ya amince amma ba haka ransa ya so ba.

5. Patricia Etteh

Patricia Etteh mace ta farko da har yanzu ta taba zama shugabar majalisar wakilai a Najeriya.

A shekarar 1999 ta wakilci mazabar Ayedaade/Isokan/Irewole daga jihar Osun da farko a karkashin  inuwar AD, amma daga baya ta sauya sheka zuwa PDP a lokacin da take neman tazarce a 2003.

A shekarar 2007 ta kafa tarihin zama mace ta farko da aka zaba shugabar majalisar.

Amma bayan watanni biyar kacal, an same ta dumu-dumu da badakalar cin hanci, har ta tilasta mata murabus.

‘Yan majalisa sun zarge ta ne da bayar da kwangilar gyaran gidanta da na mataimakinta a kan Naira miliyan 628 da kuma sayen motoci guda 12.

Ko da yake, daga baya an wanke ta daga zargin damfarar da abokan aikinta suka yi mata.

Amma har yanzu, ’yan adawa da mata suna yi mata kallon  mai cin hanci a tsakanin mata ’yan siyasa.

Yanzu haka Patricia ta kai kimanin shekaru 70 kuma ba kasafai ake ganin ta a cikin jama’a ba.

A shekarar 2022 EFCC ta kama ta kan zargin karbar Naira miliyan 130 daga wani dan kwangilar da ba a bayyana sunansa ba daga Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC).

6. Peter Odili

Peter Odili ya mulki Jihar Ribas daga 1999 zuwa 2007, kuma duk da cewa ya bar mulki, amma har yanzu akan ji duriyarsa.

Ko a kwanann nan an hango shi cikin masu goyon bayan  Gwamnan Jihar Ribas na yanzu, Siminalayi Fubara, wanda ke fama da rikicin siyasa da tsohon gwamna kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, ta jima tana farautar  Peter Odili kan badakalar wata Naira Biliyan 100.

Sai dai Peter ya ci gaba da zille wa hukumar, saboda yana zuwa kotu tana ba shi kariya daga EFCC.

7. Maryam Inna Chiroma

Hajiya Inna tsohuwar ministar harkokin mata ce tsakanin shekarar 2005 zuwa 2007 kuma tun kafin nan ta yi suna a fagen siyasa.

Ta yi Manajan Darakta na Hukumar Kula da Ruwa ta Kasa (NIWA) ta yi suna wurin samar da wakilci tare da kara yawan mata harkokin siyasa.

Hajiya Inna, tsohuwar shugabar mata ta PDP ta kasa ce, kuma ta yi burin zama mataimakiyar shugaban jam’iyyar na kasa shiyyar Arewa a 2017.

Ta sake yin wani yunkuri a karo na biyu a shekarar 2021, amma Ambasada Umar Damagun, wanda yanzu shi ne shugaban riko na jam’iyyar ya doke ta.

8. Kema Chikwe

Kema Chikwe ta yi fice a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Ta kasance daya daga cikin manyan ministocin gwamnatinsa kuma da dama sun ce tana da karfin faɗa aji a fadar shugaban kasa a lokacin.

Karan Kema Chikwe ya kai tsiko. Ita ce mace ta farko da ta taba zama ministar sufuri da jiragen sama a a Najeriya .

Ta rike Shugabar Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB), ta yi Jakadiyar Najeriya a Ireland, kuma ta taba zama Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP ta kasa.

Kema ta yi yunkurin zama gwamna da Sanata a jihar Imo amma ta sha kaye.

9. Cif Olu Falae

Olu Falae ya zamo sananne ne saboda kwazon da ya nuna a lokacin daidaita tsarin mulki (SAP) a karkashin gwamnatin mulkin soja ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida har aka yi masa lakabi da Mista SAP.

Ya yi aikin gwamnati kafin ya koma banki, ya yi sakataren gwamnatin tarayya, kafin ya zama minista, daga bisani ya tafi gidan yari.

Olu Falae dai ya samu nasarori da yawa a rayuwarsa kuma ya gwada sa’arsa a zaben shugaban kasa a 1999 da 2003, amma Olusegun Obasanjo na PDP ya kayar da shi.

Olu Falae ya rungumi kaddara ya koma gidansa da ke Akure, inda a yanzu ya zama basaraken gargajiya da ake wa lakabi da Olu Abo na Ilu-Oba kuma Baba Oba na masarautar Akure.

10. Sarah Jibrin

Sarah Jibrin, ta yi takarar shugaban kasa, kuma har yanzu Sarah na ci gaba da cewa mata ba sa goyon bayan mata masu neman mukaman siyasa.

Ita ce mace ta farko da ta tsaya takarar shugabancin Najeriya har sau hudu.

Haka kuma ita ce mace daya tilo da ta tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Muƙamin da ta rike a siyasance na karshe shi ne a lokacin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da aka nada tai mai ba shi shawara ta musamman kan da’a da kimar kasa.

Wadannan na daga cikin manyan ’yan siyasa da a yanzu ba a cika jin duriyarsu ba. Wasu lokaci ya tafi ya bar su.