Kungiyar Manyan ’Yan kasuwar Man fetur ta Najeriya (MOMAN) ta bayyana niyyarta ta sayen tataccen man fetur daga Matatar Dangote.
Matatar ta Dala biliyan 15 da ake dab da kammala ta a Legas ana sa ran za ta rika tace litar man fetur miliyan 50 a kullum.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, wannan bayani yana kunshe ne a wata sanarwa da Rukunin Kamfanonin Dangote ya fitar a makon jiya.
Sanarwar ta ce ’yan kasuwar sun bayyana haka ne a ziyarar da suka kai kwanakin baya a harabar matatar da ke Ibeju-Lekki a Legas.
A yayin ziyara, Shugaban Kungiyar MOMAN, Mista Adetunji Oyebanji, ya ce matatar za ta taimaka wajen magance matsaloli da dama da suka shafi shigo da albarkatun man fetur zuwa kasar nan.
Mista Oyebanji ya yi fatan Matatar Dangote za ta bayar da cikakkiyar dama ga mambobin Kungiyar MOMAN su gyara tare da inganta harkokin man fetur kuma matatar ta fitar da Najeriya daga kasa mai shigo da man fetur zuwa mai dogaro da kanta wajen tace albarkatun man.
Ya ce, “Wannan matata za ta fitar da mu daga kasar da ta dogara wajen shigo da man fetur zuwa mai dogaro da kanta.
“Za ta mayar da Najeriya zuwa matakin da dukkan albarkatun man fetur da muke bukata su zamo a wadace wajen samar da su a cikin gida.
“Kuma za ta kasance babbar dama ta ci gaba tare da sauya al’amura gare mu kuma muna fatan ganin an kammala ta.”
Da yake mayar da jawabi Babban Jami’in Gudanarwa na Matatar Man Fetur ta Dangote, Mista Giuseppe Surace, ya shaida wa ’yan kasuwar man fetur din cewa an tsara matatar ne ta yadda za ta tace nau’o’in man fetur ciki har da man fetur da man dizal da man jiragen sama da sauransu.
Ya ce ana sa ran matatar za ta rika tace lita miliyan 50 na man fetur da lita miliyan 15 na man dizal a kowace rana, inda za ta tace tan miliyan 10.4 na fetur da tan miliyan 4.6 na dizal da tan miliyan 4 na man jirgin sama a kowace shekara.
Ya kara da cewa tana kuma da kamfanin yin takin zamani wanda zai rika amfani da abubuwan da matatar ta tace wajen yin takin zamani.