Rundunar Sojin Najeriya ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi mata na yi wa gwamnatin Shugaba Kasa Muhammadu Buhari juyin mulki saboda tarin matsalolin tsaron da suka addabi kasar.
Wannan dai ba shi ne karon farko da sojojin ke watsi da irin wadannan shawarwarin ba, sannan suke jaddada goyan bayan su ga Shugabanda kuma mulkin Dimokradiyya.
- Buhari ya sake kiran taron Majalisar Tsaro a Abuja
- An kara wa’adin hada layukan waya da NIN zuwa karshen watan Yuni
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Rundunar ta fitar mai dauke da sa hannun Daraktanta na watsa labarai, Janar Onyema Nwachukwu, ta ce sojojin za su cigaba da marawa gwamnatin baya wajen aikin samar da tsaro da kare dimokiradiya da kuma kaucewa shiga harkokin siyasa.
Daraktan ya ce yana da kyau mutane su fahimci cewar rundunonin sojin na mutunta gwamnatin da ke karagar mulki da kuma sauran bangarorin ta, kuma za su cigaba da yin hakan kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Kasar na shekarar 1999 ya tanada.
A makon jiya’yan Majalisun kasar sun bukaci shugaban kasa Buhari da ya kafa dokar ta baci kan bangaren tsaro domin kawo karshen kashe-kashen da suka addabi kasar sakamakon hare-haren ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma mayakan Boko Haram.
Buhari na taro da Manyan Hafsoshin Tsaron Kasa
A ranar Talata Shugaba Buhari ya sake kiran taron Majalisar Tsaro ta Kasa a Fadar Shugaban Kasa ta Ado Rock dake Abuja wanda aka fara yi ranar 30 ga watan Mayun 2021.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Shugaban ya kira taron ne da nufin tattauna matsalolin tsaron dake addabar kasar.
Wadanda ke halartar taron na ranar Talata kamar na makon da ya gabata sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.
Sauran sun hada da Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi da Mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da kuma Babban Sufeton ’Yan Sanda na Kasa Usman Alkali Baba.
Kazalika, Babban Hafsan Tsaron Najeriya, janar Lucky Irabor da Babban Sojin Kasa, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da Babban Hafsan Sojin Ruwa, Bayis Admiral Auwal Zubairu da Babban Hafsan Sojin Sama, Eya Mashal Isiaka Amao suma suna halartar taron
Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da kalubalen tsaro iri-iri.