Hukumar Kididdiga ta kasa (NBS) ta sanar cewa, annobar Coranavirus ta kara tsananta matsalar karancin abinci a wasu manyan birane hudu da ke fadin tarayya.
Biranen da matsalar karancin abinci ta yi wa rubdugu sun hadar da Legas, Kano, Fatakwal da kuma babban birnin kasar wato Abuja.
Hukumar ta sanar da hakan ne cikin wani sabon rahoto da fitar ranar Litinin kan mummunan tasirin da annobar cutar ta haifar a fadin kasar.
Alkaluman da hukumar NBS ta fitar sun nuna cewa, karancin abinci ya kai wani mataki na intaha a manyan biranen hudu, sai dai ya fi muni a jihar Ribas da kuma birnin Abuja.
NBS ta ce “kashi 72 da kashi 79 cikin 100 na magidanta a jihar Ribas da Abuja ba sa iya samar da wadataccen abinci da zai ciyar da iyalansu sau uku a rana.”
“Magidanta a wadannan jihohin hudu ba sa iya ware ko sisi a matsayin kudin ajiya na abinda ke shiga lalitarsu.”
“Sannan suna cin bashin kudi domin biyan wasu bukatu na yau da kullum, wanda ke kara jefa su cikin matsanancin yanayi na tattalin arziki da rage kudaden da suke adanawa domin gaba.”
Haka kuma rahoton wanda ya kunshi yanayin aiki a rubu’i na biyu na bana, ya nuna yadda aka samu raguwar ayyukan yi a jihohin nan hudu, yayin da aka kwatanta da halin da ake ciki kafin bullar annobar COVID-19 a kasar.