Shekarar 2024 ta zo da manyan kalubale a Najeriya inda aka yi fama da iftila’i da rashe-rashe da sauran abubuwa marasa dadi.
Aminiya ta kawo irin abubuwan da suka faru a shekarar nan da muke shirin bankwana da ita.
1- Ambaliyar Borno
Ambaliyar da ta auku a 2024 ita ce mafi muni a shekaru 30 da suka gabata a Jihar Borno.
Ambaliyar ta samo asali ne daga mamakon ruwan sama na tsawon kwanaki a akasarin sassan jihar, wanda ya fi kamari a kananan hukumomin Maiduguri da Jere.
A wata ranar Litinin gwamnatin jihar ta rufe makarantun firamare da sakandare domin kare dalibai daga salwanta, daga bisani da dare lamarin ya yi sanadiyyar fashewar Madatsar Ruwa ta Alau mai tazara daga garin Maiduguri, inda ruwan ya fara shida unguwanni, kafin safiya yawancinsu suna cikin ruwa, a wani yanayi da shekaru 30 rabon da ganin irinsa a garin.
Ambaliyar ta mamaye Fadar Shehun Borno da unguwannin Post Office, Gwange, Moromoro, Gadar Customs, Gidan Zoo, Bulabullin, Maidoki Roundabout, Jami’ar Maiduguri, Cocin Saint Patrick, Kofa Biyu, Fori, Galtimari, Gwange, da Bulabulin da sauaransu, da sauran wurare, lamarin da ya tilasta wa dubban jama’a hijira.
“Kowa ya kaurace wa yankin post office, kasuwar Monday Market zuwa zoo da gidan man Hissan saboda ambaliya ta riga ta shanye su, mota ba ta iya bi,” in ji Refeal, wani mazaunin Maiduguri.
“Da mislain 12:30 aka sanar da mu cewa mu kwashe ’yan kayan da za mu iya, amma kafin mu ciro takardun shaidar karatunmu, har ruwan ya kawo mana mara,’ in ji wani mazaunin Galtimari.
Bilyaminu Yusuf, ya ce, “muna cikin mawuyacin hali a Lagos Street, ambaliya ta sa mu hijira zuwa makarantar Firamare ta Galtimari mun bar kayanmu a gida.”
Wani dan kasuwa ya ce, “Duk shagunan da ke Monday Market da Post Office ruwa ya shanye su.”
Wakilinmu a garin Maidurugi ya zagaya garin, inda ya iske ’yan kasuwar Monday Market suna lissafin irin asarar da suka yi a ibtila’in, inda suka nuna matukar kaduwarsu da kuma tunanin yiyuwar maye gurbin abin da suka rasa.
2- Fashewar tankar mai A Jigawa
A shekarar ce wata tanka da ta taso daga Kano makare da man fetur zuwa garin Nguru na Jihar Yobe ta yi bindiga a Jihar Jigawa inda ta yi ajalin mutum 125 ta jikkata wasu gommai sakamakon mummunar kunar da suka samu.
An yi zargin cewa motar ta kwace ne daga hannun direban ta faɗi da misalin karfe 11 na dare a garin Majiya da ke Karamar Hukumar Taura. Bayan faɗuwar motar ne mazauna yankin da kewaye suka rika tururuwar zuwa kwalfar man da ke tsiyaya, inda aka yi rashin sa’a wuta ta tashi, ta yi bindiga ta kashe mutum 94 nan take, wasu da dama kuma da suka samu raunin kuna aka garzaya da su asibitoci.
3- Rushewar ginin makaranta a Filato
Akalla mutum 22 ne suka rasu, wasu 132 suka jikkata, galibinsu dalibai a yayin da suke tsaka a rubuta jarabawa, sakamakon ruftawar bene mai mai hawa biyu a makarantar Saint Academy da ke unguwar Busa Buji a garin Jos na Jihar Filato, a wata ranar Juma’a.
Kwamishinan Watsa Labarai na jihar Musa Ibrahim Ashoms ya tabbatar da cewa na wadanda suka jikkatan suna samun kulawa a asibitoci daban-daban a yayin da hukumomin agajin gaggawa daban-daban da jami’an tsaro ke ta fadi tashin zakulo daliban da suka makale a baraguzan ginin.
4- Bayyanar Lakurwa
A shekarar 2024 ce Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da bullar wata sabuwar ƙungiyar ta’adda da ake kira Lakurawa a jihohin Sakkwato da Kebbi, wadda ake fargabar za ta zama babbar barazanar tsaro a yankin Arewa maso Yammacin kasar.
Kakain rundunar, Manjo-Janar Edward Buba, ya ce mayaƙan suna kwararowa ne daga ƙasashen Nijar da Mali tun bayan juyin mulkin da sojojin Nijar suka yi, lamarin da ya gurgunta alaƙar soji tsakaninta a Najeriya.
Ya bayyana damuwa bisa yadda ’yan ta’addan ke ribatar rashin kyakkyawar alaƙa tsakanin kasashen, yana mai zargin wasu mazauna da ba wa ’yan ta’addan masauki saboda kyautata musu zato da suka yi gabanin gano mugunyar manufarsu.
A yayin da Gwamnatin Sakkwato ta yi ƙorafin bullar Lakurawa, mazauna ƙauyukan Jihar Borno sun bayyana fargabar kwararowar ’yan ta’adda zuwa yankunnasu sakamakon yadda dakarun sojin ƙasar Chadi suka tsananta ragargazar mayaƙan Boko Haram a gaɓar Tafkin Chadi.
5- Kisan Sarkin Gobir
Idan ba a manta ba Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa, ya mutu a hannun ’yan bindiga a Jihar Sakkwato, inda maharan suka yi masa kisan gilla tare da binne gawarsa.
Babban ɗan sarkin, Surajo Isa, ne ya sanar cewa ’yan bindigar sun sako ƙanensa amma sun yi mahaifinsa kisan gilla nasa bayan sun karɓi kudin fansa da kuma baburan da suka buƙata.
Kisan basaraken ya jawo bore da kone-konen kadarorin gwamnati a garin Sabon Birni kimanin sa’o’i uku bayan an gudanar da Sallar Jana’izar Marigayi Sarkin Gobir na Sabon Birni a fadarsa ba tare da gawarsa ba.
6- Rasuwar Janar Taoreed Lagbaja
A shekarara 2024 da muke bankwana da ita ne Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa ta Nijeriya, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, ya rasu.
Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya zama shugaban rundunar a ranar 19 ga watan Yuni, 2023, ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya yana da shekaru 56, ya bar matarsa Mariya, da ’ya’ya biyu.
Fadar Shugaban Kasa ce ta sanar da rasuwarsa ta hannun Hadimin Shugaban Kasa Kan Yada Labarai, Bayo Onanuga.
7- Rasuwar Sa’in Katsina
A 2024 Sa’in Kastina Alhaji Marigayi Amadu Na Funtuwa ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya a Asibitin Koyarwa ta Tarayya da ke Katsina yana da shekaru sama da 90.
Marigayin shi ne Sa’in Katsina na farko wanda Marigayi Sarkin Katsina, Usman Nagogo ya nada, kuma shi ne dan majalisar sarki da ya fi kowa dadewa.
Ya yi zamani da sarakunan Katsina uku, Sa Usman Nagogo, Sarki Kabir Usman Nagogo da kuma Sarki na yanzu Abdulmuminu Kabir, kuma dan uwa ne ga tsohon sojan nan, Janar Abba Siri-siri.
Ya yi tashe a harkokin siyasa tun a zaman da ya yi a kasar Saliyo kafin dawowarsa gida. Daga cikin ’ya’yan da ya bari akwai Alhaji Muntari Sa’i.
8- Rasuwar Herbert Wigwe
Tsohon Manajan Darakta kuma Shugaban Access Holdings, Herbert Wigwe ya rasu tare da dansa da wasu mutum uku a haɗarin jirgi mai saukar ungulu a Amurka a tsakanin yankin Nebada da California a daren Juma’a.
Herbert Wigwe ya rasu ne a kan hanyar zuwa Las Begas don kallon Super Bowl, wasan zakarun lig na shekara-shekara na Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFL) ta Amurka.
9- Rasuwar Ifeanyi Ubah
Shi ma Sanatan Anambra ta Kudu a Majalisar Dattawan Nijeriya, Ifeanyi Ubah, a wannan shekara ya riga mu gidan gaskiya a safiyar wata Asabar.
Makusanta sun ce sanatan na jam’iyyar APC ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Landan a Birtaniya kwana biyu bayan barin Nijeriya.
A farkon shekarar nan ce Sanata Ubah ya sauya sheka daga jam’iyyar YPP zuwa APC, inda ya bayyana sha’awar tsayawa takarar kujerar Gwamnan Anambra a 2025. Wasu rahotanni na cewa a bayan nan ya ba da gudunmawar Naira miliyan 71 ga Jam’iyyar APC a Anambra.
A watan Satumbar 2022 ya tsallake rijiya da baya yayin wani hari da ’yan bindiga suka kai wa ayarin motocinsa a hanyar ta zuwa Nnewi a Jihar Anambra.
10- Rasuwar Dattijon Kasa Jibo
A wannan shekarar ne Allah Ya yi wa ɗaya daga cikin dattijan ƙasar nan, Alhaji Muhammad Jibo, rasuwa a wata ranar Laraba sakamakon rashin lafiya a gidansa da ke Tudun Wada, Zariya, a Jihar Kaduna.
Ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya 10 da jikoki da dama.
Daga cikin ’ya’yansa akwai marigayi Yusuf Jibo, ƙwararren ɗan jarida da ya yi aiki da Hukumar Gidan Talabijin ta Ƙasa (NTA), da kuma gidan talabijin na CNN, daga baya ya zama Shugaban Hukumar Yaɗa Labarai ta Jihar Kaduna (KSMC).
Marigayin ya kasance shugaban dattijai na Tudun Wada, a Zariya kuma tsohon gogaggen ma’aikacin gwamnati ne da ya yi aiki da hukumar jiragen ƙasa ta ƙasa da Gwamnatin Arewancin Nijeriya.
Ya kuma yi aiki a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sannan ya zama babban kwamishina a hukumar EFCC kuma yana ad lambar yabo daga Gwamnatin Tarayya ta MFR.