A wani rahoto da jaridar New York Times ya yi tonon silili kan harajin Shugaban Amurka Donald Trump, inda ta bayar da hujjoji daga wasu kundaye bayanai na shekara 20 da suka gabata.
Amma Mista Trump ya yi watsi da rahoton cewa “labaran bogi ne kawai,” sai dai ya ki cewa uffan a lokacin da aka tambaye shi ko nan gaba zai ba da bayanan harajin nasa.
- Amurka za ta rage wa’adin bizar daliban kasashen waje
- Zaben Amurka: Yadda muhawarar Trump da Biden ta buge da zage-zage
- Yadda kamuwar Trump da COVID-19 za ta shafi zaben Amurka
Ta ce Trump shi ne dan takarar shugaban Amurka na farko da ya ki fitar da bayanan harajinsa cikin shekara 40.
“Trump ya yi kwangen biyan gamnati haraji, a wasu shekarun ma bai biya ba, madalla da hasarar da ya tafka da da karayar tattalin arziki a cikin shekarun.
“Donald J. Trump ya biya Dala 750 a matsayin haraji ga Gwamnatin Tarayya a shekarar da ya lashe zaben Shugaban Kasa.
“A shekararsa ta farko a fadar White House ma ya sake biyan Dala 750.
“Sa’annan ya ki biyan ko sisi a shekara 10 cikin 15 da suka gabata, galibi saboda yadda ya ke cewa yana tafka hasara fiye da abin da yake samu”, inji jaridar.
Jaridar ta ce Trump ya biya haraji ga kasashen waje fiye da yadda ya biya gwamnatin Amurka.
“A 2017 harajin da yake ba Amurka na Dala 750 bai kai da Dala 15,598 wanda shi ko kamfanoninsa suka bayar a matsayin haraji ga kasar Panama ba.
“A Indiya ma ya biya Dala 145, 400; sannan ya biya Dala 156, 824 ga gwamnatin Philippines.
“Kudadensa na cikin halin ha’ula’i, na hasarar daruruwan miliyoyin daloli da basussuka ya ci suka ja masa”, inji jaridar.
Akwai kuma binciken kudinsa da Hukumar Haraji ta Cikin Gida ke yi game da halaccin Dala miliyan 72.9 da ya yi ikirarin ya karba bayan ya bayar da rahoton ya tafka gagarumar hasara.
“Idan binciken ya gano cewa ya yi ba daidai ba, to yana iya fuskantar biyan fiye da Dala miliyan 100.”
“Ya yi ikirarin biyan Dala miliyan 72.9 daga kudin shigarsa shekara 10 suka wuce,
“Ya kuma yi ikirarin biyan Dala miliyan 72.9 daga kudin shigarsa wanda a kansu ne Hukumar Tara Harajin Cikin Gida ke bincike.
“A takaice dai, sahihan bayanan sirri sun nuna cewa daga shekarar 2010 ya yi ikirari ya biya harajin Dala miliyan 72.9 – ga matakan gwamnatocin jiha da na tarayya daga 2005 zuwa 2008, ciki har da riba”, kamar yadda ta bayyan.
Ya yi asarar Dala miliyan 26 na kudin tuntuba.
Jaridar ta ce, “Da ake bibiyar bayanan harajin Mista Trump, an bankado abin ban mamaki .
“Tsakanin 2010 da 2018, Mista Trump ya yi asarar Dala miliyan 26 kan wasu alkaluman da ba a bayyana ba na neman tuntuba kan aikacen-aikacen kamfanoninsa”, inji ta.
Ya biya haraji fiye da kima a wasu shekaru sakamakon AMT.
New York Times ta ce an kirkiro da dabarar biyan mafi karancin kudin haraji da zimmar kafa tarko ga attajirai wajen amfani da hasarar da suke cewa suna tafkawa domin su kauce wa biyan harji.
“Mista Trump ya biya a Tsarin Biyan Haraji Mafi Karanci na AMT cikin shekara bakwai daga 2000 zuwa 2017 – jimillar Dala miliyan 24.3.
“A 2015, ya biya Dala 641,931, wanda ya zama harajinsa na farko da ya biya Gwamnatin Tarayya tun shekarar 2010”, inji jaridar.
Kasuwanci da kadarorinsa sun yi mummunar faduwa.
“Kasancewarsa abin kasuwanci, (Mar-a-Lago) shi ma wata hanya ce ta samun miliyoyin daloli bayan an cire haraji cikinsu har da Dala dubu 109 DA 433”, inji New Yokr Times.