Dubban jama’a sun yi jerin gwano domin yin maraba ga tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha Manjo Hamza Al-Mustapha lokacin da ya ziyarci mahaifarsa garin Nguru a Jihar Yobe a karon farko bayan fitowarsa daga kurkuku inda aka tsare shi na kusan shekara 15.
A lokacin da tawagar Manjo Al-Mustapha da ta kunshi Minista a Ma’aikatar Kudi Dokta Yerima Ngama da Sanata Abdulkadir Alkali Jajere da Alhaji Mohammed Abacha da uwargidansa da kuma ’yarsa ta isa garin Nguru inda dandazon jama’a da suka fito daga kowane bangaren jihar da wasu jihohin makwabta saboda nuna murnarsu bisa sako shi.
A jawabinsa ga jama’ar don nuna farin cikinsa bisa nuna irin wannan kauna da karamcin da al’umma suka nuna masa a lokacin da yake garkame a hannun hukuma janar din ya ce yana sane da irin nuna damuwa da al’umma suka yi a yayin da yake tsare.
Don haka Manjo Al-Mustapha ya nuna godiya ga dukkan al’ummomin da suka rika nuna damuwarsu da maganganu a jaridu da gidajen rediyo da talabijin na gida da waje da jama’a suka rika yi bisa zaluncin da aka nuna musu.
Tawagar ta Al-Mustapha ta kai ziyara ga fadar Mai martaba Sarkin Nguru Alhaji Mustapha Ibnu Kyari don gode masa shi da al’ummar masarautar kan tausayawa da kaunar da suka nuna bisa halin da ya shiga. Daga sai suka zarce garin Gashuwa inda suka kai ziyarar ban girma ga Mai martaba Sarkin Bade, inda nan ma dubban jama’a ne suka tarbe su.
A wani labarin kuma Manjo Hamza Al-Mustafa ya kai ziyarar ban girma zuwa fadar Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, inda jama’a suka yi cincirindo a kofar fadar Sarkin domin yi ma tsohon dogarin Shugaba Abacha maraba da kuma fatar alheri.
Manjo Al-Mustapha ya je Zariya ne don nuna godiya ga Sarkin da jama’ar Zazzau baki daya da suka taimaka masa da addu’a a lokacin da yake gidan jarun, sai dai ya ki yin magana da manema labarai, kuma ko a fadar bai furta komai ba a gaban Sarkin.
A lokacin da yake jawabin maraba Mai martaba Sarkin Zazzau ya nuna farin cikinsa da kuma yi wa Al-Mustapha nasiha cewa duk abin da ya faru a rika bar wa Allah, kuma a rika tawakkalin cewa Allah ne Ya kaddara haka, kuma a rika hakuri da duk irin halin da mutum ya samu kansa a ciki, kuma mutane su tsare gaskiya wajen gudanar da duk al’amuransu.
Sarkin kuma ya shawarci jama’a su yi amfani da wannan lokaci na azumi su rika yi wa kasa addu’ar Allah Ya ba mu zaman lafiya.
Cikin wadanda suka yi wa Al-Mustapha rakiya har da Alhaji Mohammed Abacha.
Manjo Al-Mustapha ya samu gagarumar tarba a Yobe da Zariya
Dubban jama’a sun yi jerin gwano domin yin maraba ga tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha Manjo Hamza Al-Mustapha lokacin da ya ziyarci mahaifarsa garin…
